ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Sin: Kar A Bari Sabon Nau’in Ra’ayin Nuna Karfin Soja Ya Haifar Da Karin Tasiri

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
Fu Cong, China's permanent representative to the United Nations, during a United Nations (UN) Security Council meeting in New York, US, on Saturday, Feb. 28, 2026. Ayatollah Ali Khamenei, the supreme leader of Iran who dominated every aspect of the country for more than three decades as it faced off with the West, was killed Saturday after the US and Israel launched airstrikes on Iran, according to President Donald Trump. Photographer: Adam Gray/Bloomberg

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

A jiya Juma’a, zaunanen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong, ya halarci taron babban zauren Majalisar na tunawa da “ranar kundin Majalisar Dinkin Duniya”, inda ya ce, dole ne gamayyar kasa da kasa su yi kokarin kare sakamakon yakin duniya na biyu, kuma kar a bari sabon nau’in ra’ayin nuna karfin soja ya bazu, tare da haifar da karin tasiri a duniya.

Fu Cong ya kara da cewa, kasar Sin, bisa matsayinta na kasar da ta fara sanya hannu kan kundin Majalisar Dinkin Duniya, za ta ci gaba da daukar takamaiman matakai don cika alkawarinta na kare kundin Majalisar, da kokarin samar da gudunmowa ga yunkurin gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya.

Kana a wajen taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da batun kasar Congo Kinshasa, Fu Cong ya kalubalanci bangarori masu ruwa da tsaki da su tsagaita bude wuta a yankin gabashin kasar nan take. Ya ce, ya kamata kasashe daban-daban su bi dokar hana shigar da makamai cikin harabar kasar Congo Kinshasa, da cika alkawuran da suka dauka na ba da taimako wajen tabbatar da tsagaita wuta a kasar, yayin da a sa’i daya, ya kamata a girmama ikon mulkin kai, da ‘yancin kai, da kiyaye martabar yankin kasar ta Congo Kinshasa. Ban da haka, Fu ya kara da cewa, kasar Sin da kasashen Afirka, ciki har da Congo Kinshasa, har kullum suna cikin al’umma mai makomar bai daya, da huldar cude-ni-in-cude-ka. Kuma kasar Sin na kokarin aiki tare da sauran kasashe, don samar da karin gudunmowa ga yunkurin dawo da kwanciyar hankali, da raya tattalin arziki a kasar Congo Kinshasa.

ADVERTISEMENT

Ban da haka, yayin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ke tantance batun kasar Sudan. A madadin gwamnatin kasar Sin, Fu Cong ya mika shawarwari guda 4 ga gamayyar kasa da kasa, wato a tabbatar da tsagaita bude wuta a kasar Sudan, da tinkarar mawuyacin halin da ake ciki ta fuskar jin kai, da kara kokarin sulhuntawa, gami da magance bazuwar yake-yake zuwa yankuna makwabta. (Bello Wang)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Kofin Duniya

Daga 1930 Zuwa 2026: Yadda Aka Buga Wasa Na Dubu Ɗaya A Gasar Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci