ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Ware  ₦42bn Don Kula Da Lafiyar ‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Masu Ƙaramin Ƙarfi A 2026

by Sulaiman
8 months ago
Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kudirin ware Naira biliyan 42.18 domin samar da muhimman ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan Nijeriya miliyan 10 da ake ganin suna cikin masu rauni, a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka gabatar wa Majalisar Tarayya.

Wannan kuɗin na daga cikin jimillar Naira tiriliyan 2.48 da aka ware wa bangaren kiwon lafiya a kasafin kuɗin shekarar, inda aka tanadi kuɗaɗen ne domin sayen magunguna, kayan amfani a asibitoci, kayayyakin aikin likitanci, sinadaran gwaje-gwaje da kayan gwajin cututtuka, da nufin inganta samun kulawar lafiya musamman ga talakawa a faɗin ƙasar.

ADVERTISEMENT
  • Gwamnatin Katsina Ta Bayyana Dalilin Sakin Mutane 70 Da Ake Zargi Da Ta’addanci
  • ‘Yan Ta’adda 11 Sun Miƙa Wuya Yayin Da Sojoji Suka Kashe 8 A Borno

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya miƙa ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2026 ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa a watan da ya gabata, inda ya bayyana muhimman abubuwan da gwamnatin sa ta ba fifiko a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da zamantakewa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cewar bayanan kasafin kuɗin, bangaren tsaro da kariya ne ya samu kaso mafi tsoka da Naira tiriliyan 5.4, sai bangaren gine-ginen ababen more rayuwa da Naira tiriliyan 3.56, ilimi da Naira tiriliyan 3.52, sannan kiwon lafiya da Naira tiriliyan 2.48, wanda ya zama bangare na huɗu mafi girma a jerin fifikon kashe kuɗin gwamnati.

Daga cikin jimillar kasafin kuɗin Tarayya na Naira tiriliyan 58.47, kuɗin da aka ware wa kiwon lafiya ya kai kusan kashi 4.2 cikin 100. Wannan kasafin ya kunshi shirye-shirye daban-daban na rigakafin cututtuka, samar da ayyukan lafiya, sayen kayan aikin asibiti, da tallafa wa rukunin al’umma masu rauni.

A jawabinsa yayin gabatar da kasafin kudin, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin bangarorin kiwon lafiya da ilimi wajen gina jari na bil’adama, yana mai cewa babu wata kasa da za ta ci gaba fiye da ingancin mutanenta.

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana rawar da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa ke takawa wajen tallafa wa tsarin kiwon lafiyar Nijeriya, inda ya ce tattaunawa da gwamnatin Amurka ta samar da damar samun tallafin fiye da dala miliyan 500 domin aiwatar da muhimman shirye-shiryen lafiya a ƙasar.

Gwamnati
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Jirgin Dakon Kaya Mara Matuki Na “Tianma-1000” Da Sin Ta Kera Ya Kammala Tashinsa Na Farko

Jirgin Dakon Kaya Mara Matuki Na "Tianma-1000" Da Sin Ta Kera Ya Kammala Tashinsa Na Farko

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.