ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Yi Wa Mutane 6,842 Tiyata Kyauta A Kashi 17 Na Shirin Tallafin Lafiya

by Sulaiman
4 months ago
Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa, ta gudanar da aikin kula da marasa lafiya 6,842 ta hanyar babban shirin tallafin lafiya kyauta da aka tanada domin yi wa al’umma tiyata da sauran kulawar lafiya ba tare da biyan kuɗi ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an ce an fara aiwatar da shirin tun daga watan Agustan shekarar 2023 a manyan cibiyoyin lafiya da suka haɗa da Asibitin Ƙwararru na Yariman Bakura, Babban Asibitin Gusau, Cibiyar Kula da Ido ta Gusau da kuma Asibitin Farida.

Zamfara

Sanarwar ta ce, kashi na 015, 016 da 017 na shirin tallafin lafiyar an gudanar da su daga ranar Juma’a 1 ga watan Mayu zuwa Lahadi 17 ga watan Mayun 2026.

ADVERTISEMENT

A cewar gwamnatin jihar, shirin ya haɗa da yi wa marasa lafiya tiyatar ciwon ido na yanar ido, wato cataract, cututtukan kumburin mara irin su hernia da hydrocele, gyaran matsalar yoyon fitsari ga mata (VVF), tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da lafiya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, shirin na daga cikin manufofin Gwamna Dauda Lawal na magance manyan matsalolin lafiya da ake fama da su domin inganta rayuwa da walwalar al’ummar jihar Zamfara.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

“Shirin Tallafin Lafiya na Musamman da aka gyara yana ba da damar samun kulawar lafiya kyauta ga masu fama da cututtukan da suka haɗa da cataract, hernia, hydrocele da kuma gyaran matsalar yoyon fitsari ga mata,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa baya ga bayar da magani, ana amfani da shirin wajen ilmantar da jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da tsaftar rayuwa.

An bayyana cewa an gudanar da ayyukan jinyar ta hanyar amfani da tsarin tantance marasa lafiya ta fasahar sadarwa domin kai kulawar ƙwararru zuwa yankunan karkara da ƙananan birane a ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Zamfara

Sanarwar ta ce, kashi 17 da aka gudanar zuwa yanzu sun haɗa da tiyata 5,282 da kuma jinyar wasu marasa lafiya 1,200, inda aka kula da masu cututtukan kumburi da masu fama da cataract, mata masu matsalar VVF da sauran nau’o’in tiyata na musamman da na gama gari.

Gwamnatin jihar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da irin wannan tallafin lafiya musamman domin taimaka wa marasa ƙarfi da masu buƙata a faɗin jihar.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Huldar Sin Da Rasha Ba Za Ta Canja Ba Duk Da Sauye-Sauyen Da Ake Fuskanta A Duniya

Huldar Sin Da Rasha Ba Za Ta Canja Ba Duk Da Sauye-Sauyen Da Ake Fuskanta A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.