ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Noma Tsakanin Sin Da Afirka: Daga “Sari Ka Ba Ni” Zuwa ” Zamanintar Da Kansu Tare”

by Sulaiman
3 months ago
Noma

Kwanan nan, an kammala taron dandalin hadin gwiwar fasahar noma da masana’antu tsakanin Sin da Afirka na 2026 a birnin Nairobi na Kenya, inda wakilai fiye da 100 daga Sin da kasashen Afirka ba wai kawai suka tattauna kan “yadda ake noma” ba, har ma da wani muhimmin batu, wato yadda za a ciyar da bangaren gona na Afirka gaba bisa fasahohin zamani.

A yau, ina so in ba ku wasu labarai, don fahimtar sakamakon hadin gwiwar Sin da Afirka kan zamanantar da aikin noma.——Labarin shinkafa mai aureKwanan nan, Deng Ze, uwargidan marigayi Yuan Longping, wanda kuma ake kira shi mahaifin shinkafa mai aure ta Sin, ta sami kyauta ta musamman, wato wata jakar shinkafa mai aure daga kasar Guinea. A gaban jakar, an buga tutocin kasashen Sin da Guinea, kuma a bayansa akwai rubutun firaministan Guinea Amadou Oury Bah da harshen Faransanci wanda ke cewa, “Wannan jakar shinkafa mai aure kyakkyawar alama ce ta hadin gwiwar Sin da Guinea.

“A hakika, wannan jakar shinkafa ta shaida hadin gwiwar zamanantar da aikin gona tsakanin Sin da Afirka. A Guinea, masana na Sin sun kafa cibiyar noman shinkafa mai aure mafi girma a Afirka, tun daga renon iri da shuka shinkafa har zuwa sarrafa su, sun bullo da cikakkiyar fasahar noma ta zamani, inda yawan shinkafar da aka girbe karo guda ya ninka irin na gargajiya sau 3.Manoman Afirka sun ga abin da ke faruwa a zahiri, wato idan suka bi masanan Sin wajen noma, suka yi amfani da fasahohi na zamani, za su iya samun hatsi mai yawa.——Labarin Binciken zamanantar da aikin gona daga yanayin koma baya zuwa kafa cikakken tsarin samar da kayayyaki A Zimbabwe, masana na Sin sun taimaka wa mazauna wani kauye gina “gidan kaji na kyankyasa”.

ADVERTISEMENT

Wata na’urar kyankyashe kwai mai sarrafa kanta daga Sin, tana iya fitar da kajin da aka kyankyashe fiye da 2,000 a kowane wata. Nomsa Ncube, wata mazauniyar kauyen, ta ce a da tana kiwon kaji ne bisa abun da ta sani kawai, amma yanzu tana da kyakyawan tsari, ta ce, “daga aikin ciyarwa zuwa rigakafin cututtuka, kowane mataki yana da ka’ida.” Tana samun dala 320 a kowane wata, matakin da ya kyautata rayuwarta sosai.

Sai kuma a Kenya, kamfanonin Sin sun gina masana’antu, wadanda suke mayar da ‘ya’yan Avocado da aka girba zuwa man Avocado mai karin daraja, kuma suna fitar da su zuwa kasuwannin Sin, Turai da Amurka. Wannan tsarin hadin gwiwa dogaro da shigar da fasahar zamani da tsarin gudanarwa da kuma fadada tsare-tsaren masana’antu, yana yi matukar inganta ayyukan noma.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Kazalika, daga ranar 1 ga watan Mayu, 2026, Sin ta fara aiwatar da manufar soke haraji gaba daya ga kasashe 53 na Afirka da ke da huldar diplomasiyya da ita. Manoman Afirka za su iya fitar da barkono, ridi, avocado da sauran kayayyakin da suka noma ta hadin gwiwarsu da Sin bisa fasahar zamani, zuwa kasuwar Sin ba tare da biyan haraji ba. Jaridar The Herald ta Zimbabwe ta yi sharhi game da hadin gwiwar Sin da Afirka cewa, “Guntun Gatarinka Ya fi Sari ka Ba ni .” A yau, hadin gwiwar noma tsakanin Sin da Afirka ya wuce “koyar da fasaha da dabaru kawai”, a maimakon haka, ya shiga wani sabon mataki na neman zamanantar da kansu. Wannan ba wai kawai ya kara yalwaita amfanin gona da sassauta matsalar rashin kasuwannin sayar da kayayyaki ba, har ma da kare muradun manoma ta hanyar tsarin samun oda mai dorewa.

Afirka ba ta da karancin gonaki da manoma masu kwazo, abin da take bukata su ne fasaha da kimiyya na zamani da tsare-tsare masu hangen nesa da kasuwanni masu girma. Hadin gwiwar Sin da Afirka ta fannin, yana biyan bukatun Afirka, kuma yana taimakawa zamanantar da aikin gona na Afirka. Daga shinkafa mai aure zuwa tsare-tsaren masana’antu, daga noma na gargajiya zuwa fasahohin zamani, ba wai kawai matakin ya habaka yawan amfanin gona da ake samu ba, yana kuma inganta hanyoyin samar da ci gaba.(Mai zane da rubutu: MINA)

Noma
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Sace Dalibai 42:Shugabannin Uba Askira Sun Ce Hakurinsu Ya Kare

Sace Dalibai 42:Shugabannin Uba Askira Sun Ce Hakurinsu Ya Kare

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.