Hukumar Jin Daɗin Alhazai Musulmi ta Jihar Gombe ta sanya ranar 10 ga Agusta, 2026 a matsayin wa’adin ƙarshe ga dukkan maniyyatan Hajjin shekarar 2027 domin miƙa ingantattun fasfofinsu na tafiya, yayin da shirye-shiryen aikin Hajjin ke ci gaba da kankama.
Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Mohammed Mohammed, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa umarnin ya fito ne daga Babban Sakataren Hukumar, Malam Sa’adu Hassan.
A cewarsa, an umarci dukkan waɗanda suka yi rajista domin aikin Hajjin 2027 da su miƙa takardun tafiyarsu ga ofishin hukumar kafin ko a ranar ƙarshe da aka sanya domin sauƙaƙa aiwatar da dukkan takardun da ake buƙata.
Hukumar ta bayyana cewa miƙa fasfofin da wuri zai ba ta damar kammala shirya takardun maniyyata, shigar da bayanansu cikin tsarin zamani na aikin Hajji na Saudiyya, da kuma cika jadawalin lokutan da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya suka gindaya.
Hukumar ta yi kira ga dukkan maniyyatan da abin ya shafa da su tabbatar sun miƙa fasfofinsu cikin lokaci domin kauce wa duk wata matsala da ka iya jinkirta shirye-shiryensu na tafiya aikin Hajji.














