Hukumar UNESCO da ke da hedkwata a birnin Paris na kasar Faransa, ta sanar a jiya Laraba cewa, bisa shawarar kwamitin hadin gwiwa na babban birnin gine-gine na duniya, an zabi birnin Beijing a matsayin “babban birnin gine-gine na duniya” na shekara ta 2029 na UNESCO, da kungiyar gine-gine ta duniya ko UIA.
UNESCO ta bayyana cewa, Beijing yana da wadatattun gine-gine na tarihi, da kuma hangen nesa na ci gaban birni ba tare da tangarda ba, kuma an ba shi wannan suna ne saboda ya hada wadannan abubuwa biyu tare.
Birnin mai dogon tarihi, na samun ayyukan sabuntawa masu tasiri, da al’adun gine-gine masu kayatarwa, kuma hakan yana nuna cewa, abubuwan tarihi da aka gada daga kaka-da-kakanni, da kirkire-kirkire, da rayuwar al’umma na iya taimakawa juna wajen gina birane masu dadin zama.
UNESCO a shafinta na yanar gizo, ta ce idan an yi hangen nesa kan birnin Beijing a shekara ta 2029, tabbas zai jawo hankulan kasa da kasa, inda za a kara nazarin muhimmiyar rawar da gine-gine ke takawa wajen inganta rayuwar al’umma, da kiyaye abubuwan tarihi bai daya na bil’adama a nan gaba. (Amina Xu)














