ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Sau Huɗu Buhari Ya Goyi Bayan Takarar Osinbajo-Akande

by Abubakar Sulaiman
7 days ago

Tsohon mai magana da yawun tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, Mista Laolu Akande, ya ƙaryata iƙirarin da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Babachir Lawal ya yi, yana mai bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tayin mara wa Osinbajo baya a takarar shugaban ƙasa har sau huɗu kashi daban-daban gabanin babban zaɓen 2023.

Da yake mayar da martani kan wata hira da Babachir Lawal wanda a yanzu babban jigo ne a Jam’iyyar ADC ya yi inda ya yi zargin cewa Buhari bai so Osinbajo ya nemi takarar shugaban ƙasa ba, Akande ya bayyana cewa iƙirarin ƙanzon-kurege ne. Ya bayyana cewa Buhari da kansa ya tambayi Osinbajo aƙalla sau huɗu yana mai cewa, “Idan ban mara maka baya ba, wa zan mara wa baya?”, wanda ke nuna yadda tsohon shugaban ya nuna goyon bayansa ƙiri-ƙiri.

Akande ya ƙara da cewa a lokacin yaƙin neman zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar APC a shekarar 2022, Shugaba Buhari ya yaba wa Osinbajo a bainar jama’a a gaban ɗaukacin mambobin Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) kan yadda ya gudanar da kamfen ɗinsa cikin ladabi da mayar da hankali kan muhimman batutuwan ci gaba. Ya jaddada cewa shugaban da ya ɗauki wannan mataki a hukumance ba zai yiwu a ce bai so Osinbajo ya shiga fafatawar ba, sai dai ma ƙarfafa masa gwiwa da yabonsa da ya yi.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, Akande ya caccaki matsayin Babachir Lawal na yin tsokaci a kan al’amuran da suka shafi ofishin Osinbajo, yana mai nuni da cewa an tsige Lawal daga muƙamin SGF kafin a ɗauki yawancin matakan da yake magana a kai, don haka bai san abubuwan da suka wakana a cikin ofishin ba, saɓanin shi Akande da ke halartar wuraren da ake yanke muhimman shawarwari a matsayinsa na hadimin Osinbajo.

Idan za a iya tunawa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fafata a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na APC a watan Yunin 2022, inda ya zo na uku da ƙuri’u 235 a bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya lashe zaɓen da ƙuri’u 1,271 da kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da ya samu ƙuri’u 316. Wannan sabuwar gardama na zuwa ne a daidai lokacin da jiga-jigan siyasa ke ci gaba da sake lissafin tasirin tsoffin shugabannin gabanin babban zaɓen 2027.

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
  • Abubakar Sulaiman
    Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
  • Abubakar Sulaiman
    Aikin Titin Jirgin Ƙasa Na Kaduna Zuwa Kano Ya Kai Kashi 90%

MASU ALAKA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
Siyasa

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026
Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo
Siyasa

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

October 22, 2026
Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027
Siyasa

Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027

October 22, 2026
Next Post
Shugaban Kasar Botswana: Dabarar Raya Kasa Ta Sin Abar Koyi Ce

Shugaban Kasar Botswana: Dabarar Raya Kasa Ta Sin Abar Koyi Ce

LABARAI MASU NASABA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.