ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Yanzu Burina Bai Cika Ba A Waka —Hadiza Maikano

by Rabi'at Sidi Bala
3 weeks ago
Maikano

Shafin da ke zakulo muku fitattun jaruman finafinan hausa manya da kanana, har ma da mawaka, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wata bakuwar ta musamman, wacce ta shafe tsahon shekaru masu yawa a harkar waka, wato, HADIZA MUSA wacce aka fi sani da HADIZA MAIKANO. Inda ta bayyanawa masu karatu dalilin da ya sa har ta tsunduma harkar waka, haka kuma mawakiyar ta bayar da shawarwari ga masu yunkurin fara waka, har ma da wasu batutuwan masu yawan gaske da suka shafi rayuwarta da kuma sana’ar waka.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki.

ADVERTISEMENT

Sunana Hadiza Musa, amma an fi sanina da Hadiza Maikano.

Ko za ki iya fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

LABARAI MASU NASABA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

An haife ni a garin Kano, na girma a Adamawa nayi karatu a Adamawa. Mahaifina dan Kano ne, mahaifiyata ‘yar garin Gombe ce.

Me ya ja hankalinki har ki ka fara waka?

Ban taba tunanin zan harkar waka ba, daga zuwa kai ziyara ‘studios’ din waka da ganin ‘yan finafinan hausa, daga nan na tsinci kaina a harkar waka. Inda na ce musu bari na gwada kuma na dan gwada suka ji, “Ah! wannan ai kadara ce ba za a barta ba, muryarta ta yi mana”. Aka ce to, a je a gano gidanmu, saboda duk lokacin da za a yi waka sai a je a dauko ni, a lokacin ma ba waya, sai waya dai amma ba tafi da gidanka. Mun kai ziyara ‘RK Studio’ da nan Iyantama gurin Dan’Azumi Baba (Kamaye), a hannunsa na fara waka a lokacin gaskiya.

Za ki yi kamar shekara nawa kina waka?

A yanzu a kalla zan kai kusan shekara Ashirin da hudu haka ko da biyar.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance a wancen lokacin?

Lokacin da na fara waka a gidanmu ba a sani ba, lokacin da aka riga aka sani kuma na riga nayi nisa. Saboda ba na fita in yi dadewar da za a gane ga inda na je, kuma ina zuwa makaranta a lokacin ina zuwa “Health and Technology”, kuma ba kullum nake zuwa wakar ba. A lokacin ba a yawan yin wakokin kamar yadda ake yi a yanzu, idan suka shirya wakar za su kira ni ne sai in sauri na je nayi shi cikin gaggawa na dawo yadda ba za a gane na je nayi na dawo ba.

Ya batun iyaye lokacin da suka fara sanin kina waka, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su?

An yi maganganu dole za a yi ta maganganu, irin “ah! wance ta fara waka, ah! harkar fim wance take” da dai sauransu. An yi maganganu daga baya kuma da aka yi dole za a hakura a yi shuru.

Da wanne mawaki ko mawakiya ki ka fara yin waka, kuma kin fara ne da amshi ko da rubutacciyar wakar da ki ka rubuta?

Gaskiya ba da amshi na fara waka ba, wakar fim ce muka fara yi tare da wani mawaki wanda ake kira da Sammani Sani Gwale (Ya sayyadi), a lokacin gaskiya da shi na fara waka a nan wajen Dan’azumi Baba ‘RK Studio’ dake Sabon Titi.

Lokacin da za ki fara rubuta waka ta kanki, shin kin samu taimakon wani ko wata, ko kuwa da kanki ki ka rubuta kuma ki ka rera?

Fitar da kari a waka ni ba ya ban wahala, abin da ma yake dan ban wahala a waka shi ne, rubutawa shi ma wajen fitar da kafiyoyi shi ne yake ban ‘problem’. Lokacin da na fara rubuta waka da kaina gaskiya ba wanda ya rubuta min, da kaina nayi jagwalgwalona na rubuta, kuma an ji ta dan ta fim ce.

Kin yi wakoki sun kai kamar guda nawa?

Wallahi ban san iya adadin wakokin da na yi ba, suna da yawa gaskiya, saboda a lokacin daga baya an zo ana yin wakoki sosai, ka wuni ana waka ban san iya adadin wakokin da na yi ba. Tunda a lokacin ba kowane gari bane ake da ‘studio’ Kano ne, kusan duk sauran garuruwan da ke tsallake kusa da mu din nan Kano ake zuwa a zo a yi, kuma idan an zo mu ne dai a ‘studio’ za a tarar a baka aiki ka yi, muna ayyuka sosai gaskiya.

Ko za ki iya fadowa masu karatu sunayen kadan daga cikin wakokin da ki ka rera ko ki ka rubuta?

Wakar da aka fi gane ni da ita, ita ce Mantega, wacce muka yi da Yakubu Muhammad. Wakokin fim din jarida “Adamcy Kazo, Jamila ta iya daura zani, Ranar Guda, Saran Kada Talle za ki sa na daka tsalle da Abbakar Sani, sai Dan Soja Soja taho dan mu shana, da Yakubu Muhammad, Jamila Ta Iya Daura Zani da Sani Danja muka yi. da Ayye Lajiga-Lajiga Lajiga Ayyeh Lajiga oh! oh!!, da Ranar Murna Gimbiya ta hau dokin girma, da Agogo yana latti eh, eh. da Mui Walwala cikin murna, suna da yawa kadan dai daga ciki kenan.

A cikin wakokin da ki ka rera ko ki ka rubuta wacce waka ce ta zamo bakandamiyyarki, kuma me ya sa?

Kusan Man Tega din dai, ita ce bakandamiya ta, kuma ita ma tana dauke da tarihi sosai. A lokacin da aka yi ta, gaskiya a lokacin ana ganiyar yin wakoki, kuma ni ma ina cikin wani yanayi na soyayya a lokacin. To, shi ya sa duk lokacin da aka tambaye ni abu akan wakar a lokacin yanayinta to, nakan tuno da lokacin duniya tana kwance ba irin yanzu bane, ba ka da wani ‘problem’ ba ka da ‘pressure’. Tun ranar da aka buga ta wakar take tashe kuma har yau.

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta sanadiyyar waka?

Duk abin da mutum zai yi a rayuwa ai sai ya samu kalubale, akwai an sassamu kuma da izinin Allah an tsattsallake, ai ba abin da yake tabbatacce.

Wane irin nasarori ki ka samu game da waka?

Gaskiya an samu nasarori tunda an samu daukaka, an samu abubuwan rayuwa na yau da gobe irin su; Gida, Mota, Hajji, duk wata sutura da Allah yake wa bawa ya min a cikin waka, dan haka ba abin da zan cewa sana’ar waka sai dai na ce ma sha Allah. Yadda muka fara lafiya Allah ya sa mu gama lafiya, amfanin da yake ciki Ubangiji Allah ya sada mu da shi. Sharrin da yake ciki da wasu kaddarori munana ubangiji Allah ya tsare mu.

Kin yi wakoki a baya daga bisani kuma sai aka ji ki shuru, shin me ya faru, kuma har yanzu kina ci gaba da yin waka ko kuwa kin dakata da yi?

Lokacin da nake tsaka da yin wakoki kuma nake tashe na a lokacin nake samun kudi kuma ake yayi na a lokacin na tafi nayi aure, yanzu nayi aure ina da yarana guda uku, amma kuma yanzu ba ni da aure. Kuma na dawo ina ci gaba da waka ta a halin yanzu.

Ko akwai wani ci gaba da aka samu ko rashin ci gaba a fannin waka wanda ki ke ganin ya wanzu a yanzu sabanin lokutan baya?

Mawakan yanzu da na ‘da’ gaskiya akwai daraja da soyayyar juna, kuma duk inda mawaki yake idan ya je za ka ga tsakaninshi da masoyi shi babu hijabi, akwai alaka me kyau suna sonka, kana son su, kuma kana shiga cikinsu. Sabanin yanzu wani in daukaka ta zo mishi yana ganin kawai in ba wanda za su bashi wani abun duniya ba kawai to, ba masoyinshi bane. Za a nemi daukakar a nemi jama’ar amma kuma wani lokaci kusan dai yanzu gaskiya kwadayi ya fi yawa a ciki, an fi ga abin da za a bayar. Amma ‘da’ din an fi son masoyan ma, kana so ka ga fans dinka kuma ka ga ana yin ka. Yanzu kuma mutane mawaka yanzu sun fi lura ga abin da za su samu.

Mene ne burinki na gaba game da waka ko kuma mawaka?

Har yanzu burina bai cika ba a waka, kullum ina fada ina da buri a waka wanda Allah kadai ya san me ke cikin raina, wanda ina burin Allah ya kai ni wannan matakin. Akwai ‘target’ dina gaskiya, amma dai har yanzu ban samu na kai wannan ‘target’ din ba. Duk ranar da Allah kuma ya sa na kai zan fadawa ‘yan jarida na ce to, yau kaza ne da kaza da kaza nake so, kuma yau Allah ya nuna min.

Wace ce babbar kawarki a cikin mawaka?

Mawaka kawayena ne, kowa kawata ce.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga harkar waka?

Shawara ita ce, hakuri idan ka yi hakuri ko an cuceka waka tana da halacci, wallahi ko an cuceka a tafi- a tafi sai an dawo watarana sai ka mora. An yi mana an yi mana kuma mun mora, mun yi hakuri mun ga ranar sa, an cuce mu mun ga ranar sa. Dan haka waka wata aba ce wacce take da halacci, idan kuma ka yi mata butulci sai ta yi maka butulci, saboda na ga mawakan da suka ci da waka suka rayu da waka, suka yi arziki da waka daga baya suka zo suka ce sun daina suka kushe waka, suka ci mata mutunci, suka shiga cikin jarida ‘yan jaridu da rediyo suka ci mata mutunci daga karshe kuma sun dawo ciki. Allah shi ne yake ajjiye bawa a duk inda ya so, ranar da ya ga damar canja maka sana’a ba tare da ka fito ka cika baki ka ce wani abu ba sai dai a ga baka ciki, Allah ya canza maka da abin da ya fi wannan alkhairi. Amma idan Allah bai so ba ko kuma rabonka bai kare a wuri ba, babu yadda ka iya ko ka zaga sai ka je ka dawo, to, dan haka waka tana da halacci, idan ka yi mata butulci kuma tana ramawa. Ni ban taba ganin ma ain da yake sakayya cikin gaggawa ba irin harkar waka.

Idan mutum yana so ki yi masa waka ta wacce hanya zai bi?

Akwai lambar wayata da nake bayarwa, wanda idan ana nemana indai aiki ne za a yi min ‘message’ ko in an kira in sha Allahu zan amsa.

Me za ki ce da masoyanki, masu sauraron wakokinki?

Ina son masoyana kamar yadda suke so na, kuma ina yi musu fatan alkhairi, kuma a ci gaba da hakuri da mu.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina gaida ubangidana Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, da Alhaji Abubakar Malam Shattiman Gandu, da sauransu.

Maikano
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A 29-05-2027
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

MASU ALAKA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
Nishadi

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

May 31, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Nishadi

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

May 23, 2026
Bayan Harkar Fim, Sayar Da Abinci Ne Babbar Sana’ata – Aisha Yola
Nishadi

Bayan Harkar Fim, Sayar Da Abinci Ne Babbar Sana’ata – Aisha Yola

May 10, 2026
Next Post
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwar Masu Bayyana Ra’ayoyi Ga Sabon Salon Sin Da Amurka Na Kara Daidaita Dangantakarsu

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwar Masu Bayyana Ra’ayoyi Ga Sabon Salon Sin Da Amurka Na Kara Daidaita Dangantakarsu

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.