Aƙalla sojoji biyu da wani ɗan ƙasar Sin (China) ne aka kashe, biyo bayan wani mummunan hari da mayaƙan ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa suka kai a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin kwanton-ɓauna ne kan tawagar dakarun sojojin da ke ba da kariya ga ma’aikatan ƙasar Sin da ke gudanar da ayyuka a yankin. Ƴan ta’addan sun buɗe wuta kan jami’an tsaron, inda aka yi musayar wuta mai zafi da ta yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu da ɗan ƙasar Sin ɗin a take, kafin maharan su tsere cikin daji.
Bayan faruwar harin, an tura ƙarin dakarun sojoji tare da haɗin gwiwar jami’an Ƴansanda zuwa yankin, don kwashe gawarwakin mamatan, da kuma bin sawun ƴan ta’addan da suka tafka ɓarnar zuwa maɓoyarsu a dazuzzukan da ke kan iyaka.
Wannan farmaki na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen ɓarkewar ayyukan sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa a jihohin Kebbi da Sokoto, lamarin da ya sa shugabannin tsaro suka lashi takobin tsananta hare-haren kakkabe mayakan ƙungiyar a duk faɗin yankin Arewa maso Yamma.













