Gwamnatin Tarayya na shirin sanya ƙayyadadden farashi (price cap) a kan kuɗin saukar man fetur a tashoshin ruwa (landing cost) a kan Naira 1,350 ga kowace lita, a matsayin wani ɓangare na matakan daƙile ƙarin tashin farashin mai a gidajen mai da kuma sauƙaƙa matsin tattalin arziƙi.
Wannan mataki ya biyo bayan tattaunawa tsakanin hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a fannin mai, karkashin Hukumar Kula da sashin Albarkatun Man Fetur da Iskar Gas ta Ƙasa (NMDPRA), tare da haɗin gwiwar Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) da ƙungiyoyin dillalan mai (irin su MEMAN da IPMAN).
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a shawo kan ƙalubalen hauhawar kuɗin saukar man da sauyin darajar kuɗaɗen ƙasashen waje ke haifarwa.
A ƙarƙashin tsarin da ake shirin aiwatarwa, gwamnati na duba dabarun samar da sauƙi ta fannin haraji da rage kuɗaɗen caji a tashoshin ruwa, da kuma daidaita tsarin canjin kuɗin waje domin tabbatar da cewa ainihin kuɗin shigo da man bai zarce Naira 1,350 a kowace lita ba. Wannan mataki na da nufin hana ƴan kasuwa ƙara farashin lita zuwa matakan da za su jefa ƴan ƙasa cikin ƙuncin rayuwa.
Masu ruwa da tsaki a harkar man fetur sun bayyana cewa matsin lambar da ake fuskanta wajen neman dalar Amurka da tsadar jigilar man a tekun duniya su ne manyan dalilan da suka sa kuɗin saukar man ke ci gaba da ƙaruwa.
Sun jaddada cewa samar da mafita ta dindindin zai dogara ne a kan wadatar man da ake tacewa a cikin gida ta hanyar manyan matatun man ƙasar, domin rage dogaro da shigo da shi daga ƙetare.
Wannan yunƙuri na zuwa ne a yayin da ƴan Nijeriya ke ci gaba da fuskantar matsanancin halin tsadar rayuwa da tashin farashin sufuri, inda gwamnatin ke ƙoƙarin kare kasuwar man daga faɗawa cikin rikicin da zai tilasta ƙarin farashi a faɗin ƙasar.














