ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kano Ta Kashe Biliyan 928 A Ayyukan Ci Gaba 1,508

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kashe sama da Naira biliyan 928 wajen aiwatar da ayyukan ci gaba 1,508 a ƙananan hukumomi 44 na jihar tun bayan hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf kan mulki. A cewar gwamnati, an kammala ayyuka 799, yayin da 709 ke ci gaba da gudana a matakai daban-daban.

Kwamishinan Ma’aikatar Saye da Kwangiloli ta Jiha, da Bibiyar Ayyuka da Tantance Su, Kwamared Nura Ma’aji Sumaila, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kan ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa. Ya ce ayyukan sun shafi muhimman fannoni da suka haɗa da gina da gyaran hanyoyi, da inganta birane, da sufuri, da ilimi, da lafiya, da samar da ruwan sha, da tsaro da sauran ayyukan jama’a. Ya kuma bayyana cewa adadin bai haɗa da ayyukan mazabu 619 da ‘yan majalisar dokokin jihar ke aiwatarwa a faɗin ƙananan hukumomin Kano ba.

Sumaila ya ce gwamnatin ta bayar da kwangilolin da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 169 domin ayyukan inganta birnin Kano, ciki har da gyaran hanyoyi, gina magudanan ruwa da sauran ayyukan more rayuwa. Haka kuma, gwamnati na gina hanyoyi masu tsawon kilomita biyar a ƙananan hukumomi 38 ƙarƙashin kwangilolin da suka haura Naira biliyan 118, domin inganta zirga-zirga da bunƙasa tattalin arziƙin yankunan karkara.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa gwamnatin ta amince da kwangilolin da suka haura Naira biliyan 6.8 domin gina ofisoshin rundunar Neighbourhood Watch a ƙananan hukumomi 36, da nufin ƙarfafa tsaron al’umma. A cewarsa, ayyukan raya karkara da suka shafi ilimi, lafiya da sauran muhimman abubuwan more rayuwa a faɗin jihar sun kai sama da Naira biliyan 397, yayin da wasu ayyukan da ke gudana suka zarce Naira biliyan 255.

Ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ingancin ayyuka ta hanyar sa ido mai tsauri domin tabbatar da an yi amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 9, Sun Sace Da Dama A Birnin Gwari

Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 9, Sun Sace Da Dama A Birnin Gwari

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.