ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hijira: Malaman Musulunci Sun Buƙaci  Musulmi Su Yi Riƙo Da Gaskiya Da Adalci

by Sulaiman
3 months ago

A yayin da al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke shiga sabuwar shekarar Musulunci (Muharram, 1448H) a ranar Talata, Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci, reshen Jihar Ogun, ta yi kira ga mabiya addinin Musulunci a faɗin ƙasar nan da su sadaukar da rayuwarsu, wajen tabbatar da adalci, riƙon amana, mutunta Ɗan’adam da sauran kyawawan ɗabi’un da ake buƙata cikin gaggawa, domin samar da zaman lafiya a duniya.

Dangane da zaman lafiya, haɗin kai da haƙuri da wahalhalu, ƙungiyar ta ce; ya kamata Musulmin Nijeriya, su yi nazari kan al’amuran zamantakewa da siyasa na wannan lokaci, “yayin da ɗaiɗaikun mutane da al’ummomi ke fuskantar ƙalubale da dama”.

Da yake jawabi a taron manema labarai na duniya a ranar Talata a Abeokuta, babban birnin jihar, Shugaban PMC, Alhaji Abdul Wasiu Akinyemi, ya ce; ƙa’idojin Hijira na nan daram a yau. Don haka, masu bin addinin Musulunci na buƙatar su yi tunani a kan darussan da za su bayar, su ba da tasu gudummawar wajen gina al’ummar Nijeriya “mafi zaman lafiya, daidaito da kuma wadata”.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana cewa, Hijrah wata dabara ce ta ruhi da zamantakewa da siyasa, wacce ta kafa tushen samar da al’umma mai adalci da wadata, Akinyemi ya yi kira ga masu bin addinin Musulunci da su tabbatar da cewa, suna gudanar da adalci da riƙon amana da kuma mutunta Ɗan’adam kowa da kowa a Nijeriya, yana mai jaddada cewa; “babu wata al’umma da za ta ci gaba, ba tare da kwatanta gaskiya da adalci ba”.

“A matsayinmu na ƴan ƙasa kuma shugabanni, dole ne mu bayar da shawarar tabbatar da gaskiya a cikin shugabanci, riƙe amana a ofisoshin gwamnati, kare haƙƙin bil’adama, rarraba albarkatun ƙasa, bin doka da oda da kuma aiwatar da adalci a zamantakewa. Babu wata al’umma da za ta ci gaba, ba tare da kwatanta gaskiya da adalci a tsakaninta ba”.

LABARAI MASU NASABA

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

“A cikin al’ummominmu daban-daban, ya kamata musulmi da gangan su inganta tattaunawa tsakanin addinai, zaman lafiya, mutunta bambance-bambancen al’adu, haɗin kan ƙasa da zamantakewar al’umma.

Rarrabuwa tana raunana al’umma, yayin da haɗin kai yake ƙarfafa su”.

Shugaban na PMC ya kuma yi kira da a ƙara saka jari a fannin ilimi mai inganci, koyon sana’o’i, kasuwanci, hada-hadar jama’a, da kuma inganta tarbiyyar matasan Nijeriya, bisa la’akari da muhimmancin yawan jama’arsu da kuma ɗimbin ƙarfin da suke da shi.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa

MASU ALAKA

Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Sakamakon Ziyartar Kasar Sin Sau 13 Shugaban Myanmar Na Da Mahanga Dangane Da Salon Zamanantarwa Irin Ta Sin

Sakamakon Ziyartar Kasar Sin Sau 13 Shugaban Myanmar Na Da Mahanga Dangane Da Salon Zamanantarwa Irin Ta Sin

LABARAI MASU NASABA

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.