A yau Litinin 24 ga wata, hukumar kula da ci gaban kasa da gyare-gyare ta Sin (NDRC) ta kebe kudi na gaggawa, da ya kai yuan miliyan 50 daga cikin kudaden zuba jari da ke cikin kasafin kudin gwamnatin tsakiya, domin tallafa wa kokarin jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta wajen ayyukan farfadowa na gaggawa, bayan abkuwar ibtila’o’in mahaukaciyar guguwa da kuma ambaliyar ruwa.
Za a yi amfani da wadannan kudade ne musamman wajen gaggauta maido da kayayyakin more rayuwa da suka lalace a yankunan da abin ya shafa, da suka hada da hanyoyi, da wuraren kula da al’amuran ruwa, da kuma cibiyoyin hidimta wa rayuwar jama’a kamar makarantu da asibitoci, domin bai wa al’umma damar komawa rayuwar yau da kullum da harkokin samar da kayayyaki cikin hanzari.
A kwanan baya dai, sakamakon mahaukaciyar guguwar Narra ta 19 da aka yi a wannan shekara, wurare da dama a jihar Guangxi, ciki har da Chongzuo da Fangchenggang, sun fuskanci ruwan sama mai karfi a-kai-a-kai tare da ambaliyar ruwa mai tsanani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














