Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bai wa jam’iyyun siyasa wa’adin zuwa ranar 24 ga Oktoba, 2026, domin sanar da ita idan suna ganin an cire sunayen ’yan takararsu ba bisa ƙa’ida ba daga jerin sunayen ’yan takarar gwamna na zaɓen 2027.
Matakin na INEC ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da cewa wajibi ne jam’iyyun siyasa su miƙa wa hukumar rajistar mambobinsu bisa tanadin doka kafin su cancanci tsayar da ’yan takara a zaɓe.
Kwamishinan INEC kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar.
Ya ce hukumar ta yi amfani da hukuncin Kotun Ƙoli wajen kammala jerin sunayen ’yan takarar gwamna, inda ta cire jam’iyyun da suka gaza bin tanadin Sashe na 77(5) zuwa (7) na Dokar Zaɓe ta 2026.
Kotun Ƙolin ta yanke hukuncin ne a ranar 24 ga Satumba, 2026, a shari’ar INEC da Jam’iyyar Zenith Labour Party, mai lambar SC/CV/495/2026.
Hukuncin ya soke matsayar Kotun Ɗaukaka Ƙara wadda ta soke wasu tanade-tanaden dokar da suka wajabta miƙa rajistar mambobin jam’iyya a matsayin sharadin gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani.
Kotun Ƙolin ta tabbatar da cewa tanade-tanaden sun yi daidai da kundin tsarin mulki kuma wajibi ne dukkan jam’iyyun siyasa su bi su.
Haka kuma, kotun ta tabbatar da sahihancin jadawalin INEC da ya buƙaci jam’iyyun siyasa su miƙa rajistar mambobinsu tsakanin ranar 21 ga Afrilu da 10 ga Mayu, 2026.
A cewar hukumar, jam’iyyar da ta gaza cika waɗannan sharudda ba za ta cancanci tsayar da ɗan takara a zaɓen ba.
Haruna ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bisa tanadin Sashe na 287(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, wanda ya wajabta bin hukuncin kotuna.
Ya kuma bayyana cewa INEC ta riga ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar 12 ga Satumba, 2026, kwanaki 13 kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin.
Dangane da matakin da jam’iyyun da abin ya shafa za su iya ɗauka, Haruna ya ce Sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya bai wa jam’iyyun da ke ganin an cire sunayen ’yan takararsu bisa kuskure damar sanar da hukumar cikin kwanaki 14 daga ranar da aka wallafa jerin sunayen.
Ya ce wa’adin sanar da hukumar zai ƙare ne a ranar 24 ga Oktoba, 2026.
Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da gaskiya, bin doka da kuma sahihancin tsarin zaɓe a Nijeriya.














