An gudanar da ayyukan tiyata kyauta ga maza da mata har mutum 200 daga garuruwa daban-daban na Ƙaramar Hukumar Faskari da ke Jihar Katsina a asibitin Shema, inda Injiniya Murtala Ibrahim Sheme ya ɗauki nauyin gudanar da ayyukan da waɗanda ke fama da matsalolin lafiya daban-daban.
Aikin tiyatar ya haɗa da cire gwaiwa da gyaran hainiya (hernia) da sauran matsalolin lafiya da ke buƙatar kulawar tiyata. Wannan taimako ya kasance wata babbar dama ga marasa lafiya, musamman waɗanda ba su da halin ɗaukar nauyin kuɗin jinya da tiyata da kansu.
Wannan gagarumin tallafi bai tsaya ga wani gari guda ba, maza da mata daga garuruwa daban-daban na faɗin Ƙaramar Hukumar Faskaria Jihar Katsina, ne suka samu damar amfana da wannan tallafi.
Daga cikin waɗanda suka samu tallafin sun haɗa da Abdulsamad Umar daga Faskari da Abubakar Bishor daga Faskari da Yahaya Musa daga Daudawa da Magaji Audu daga Maigora da Sa’ade Ibrahim daga Maigora da Bahari Musa daga Dan Murai da Haruna Yakubu daga Ruwan Godiya da Hadiza Balarabe daga Yankara da dai sauran bayin Allah da suka samu damar cin gajiyar wannan taimako.
Wannan tallafi ya zo ne a wani muhimmin lokaci, inda wasu daga cikinsu ke buƙatar tiyata amma ba su da ikon ɗaukar nauyin kuɗin jinya da kansu.
Ɗaukar nauyin irin wannan aiki na kiwon lafiya na daga cikin ayyukan da ke da matuƙar tasiri a rayuwar al’umma. Domin a lokuta da dama, kuɗin tiyata da sauran kuɗaɗen jinya kan zama babban ƙalubale ga marasa ƙarfi.
Ta hanyar wannan tallafin, an bai wa mutane masu yawa damar samun kulawar da suke buƙata ba tare da fuskantar nauyin kuɗin tiyata su ba.
Injiniya Murtala ya nuna cewa taimakon al’umma bai kamata ya tsaya ga magana kawai ba, ya kamata ya kasance aiki, sadaukarwa da ƙoƙarin inganta rayuwar jama’a.
Wasu daga cikin mutanen da suka samu aikin tiyatar, da kuma jama’ar da suka shaida wannan taimako, sun bayyana godiyarsu tare da addu’ar Allah ya saka wa Injiniya Murtala da alheri.
Haka kuma, wasu daga cikin waɗanda ba su samu damar shiga wannan karon ba, na ci gaba da fatan samun irin wannan dama a nan gaba.
Aikin tiyatar ya gudana ne ƙarƙashin kulawar Ismail Yusif Sheme (AS) da Ahmad Iliya Sheme da Abubakar Musa, tare da sauran waɗanda suka ba da gudunmawa wajen ganin an gudanar da aikin cikin tsari.














