Jakadan Sin A Jakadan kasar Sin a tarayyar Najeriya Yu Dunhai, ya halarci taron kasa da kasa na karawa juna sani, game da kawar da daukacin harajin fito da Sin ta fara aiwatarwa, wanda ya gudana a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya a ranar Juma’a 14 ga watan nan.Taron mai taken “Manufar kawar da daukacin harajin fito ta Sin ga kasashen Afirka, da aiwatar da sauyin salon tattalin arziki a nahiyar”, ya samu halartar karamin ministan ma’aikatar aikin gona da samar da isasshen abinci na Najeriya Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar jakada Dunoma Umar Ahmed, tare da wasu manyan jami’an gwamnati, da wakilan masarautun gargajiyar kasar.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, jakada Yu ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanar da manufar kawar da karbar daukacin haraji kan hajojin kasashen Afirka masu huldar diflomasiyya da Sin, matakin da ya kasance muhimmin jigo na gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani daga dukkanin fannoni.
Kazalika, cikin watanni uku da rabi da suka gabata, tun bayan fara aiwatar da manufar, kyakkyawan tasirinta ya fara bayyana cikin sauri, inda take kara ingiza hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka. Jakadan ya kara da cewa, Sin a shirye take ta yi amfani da cikakken tasirin manufar janye harajin, wajen yin aiki kafada-da-kafada da Najeriya da ma dukkanin sauran kasashen Afirka, wajen bude sabon babin raya hadin gwiwa tsakaninta da Najeriya da tsakaninta da kasashen Afirka.
Daga bangaren Najeriya kuwa, jami’an kasar sun jinjinawa manufar kawar da harajin, suna masu fatan daidaita manufofin samar da ci gaba tare da Sin, da bunkasa sarrafa hajoji a cikin gida, da habaka cin gajiyar manufofi, da ingiza daga matsayi, da kyautata hadin gwiwa na zahiri tsakanin Sin da Najeriya. (Saminu Alhassan)














