ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’an Tsaro Sun Hallaka ’Yan Bindiga 17 Bayan Daƙile Hari A Hanyar Gusau–Funtua

by Sulaiman
2 weeks ago
Jami’an tsaro

Akalla ’yan bindiga 17 ne jami’an Rundunar ’Yansandan Jihar Zamfara tare da sojoji suka hallaka yayin wata musayar wuta mai zafi da suka yi a kan babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne bayan wasu gungun ’yan bindiga masu yawa sun tare hanyar kusa da kauyen Unguwar Chida da ke Karamar Hukumar Tsafe, inda suka bude wa motocin da ke wucewa wuta.

A cewar wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yansandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar da yammacin Laraba, harin ya faru ne da misalin karfe 4:05 na yamma a ranar 25 ga Agusta, 2026.

ADVERTISEMENT

‘Yan bindigar sun tare motocin haya guda biyu, wato wata motar Sharon da kuma motar bas ta Hukumar Sufuri ta Jihar Sakkwato (SSTA) mai lambar rajista LV 94.

Motar Sharon, wadda Alhaji Halilu Namadi daga kauyen Taloka da ke Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto ke tukawa, tana kan hanyarta ne daga Sokoto zuwa Gwagwalada, Abuja. An harbe direban har lahira, lamarin da ya sa motar ta yi ta hantsalawa. Fasinjoji shida, maza hudu da mata biyu, sun rasa rayukansu a harin.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cikin motar SSTA da ke dauke da fasinjoji 18 zuwa Kaduna da Abuja, an harbe fasinja guda daya har lahira, yayin da wasu tara suka samu raunukan harbin bindiga.

Daga bisani, ’yan bindigar sun yi awon gaba da fasinjoji takwas zuwa cikin daji.

Bayan wasu sa’o’i, da misalin karfe 6:45 na yamma, wannan gungun ’yan bindiga ya sake kai hari kauyen Magazu da ke Karamar Hukumar Tsafe. Wani mutum mai shekaru 35, Lawali Mu’azu, ya samu rauni sakamakon harbin harsashi, kuma a halin yanzu yana karbar magani a Babban Asibitin Tsafe.

A wani samame na gaggawa da ya biyo bayan harin, jami’an ’yansanda da sojoji sun bi sahun ’yan bindigar da suka tsere zuwa hanyar Funtua–Gusau, inda suka yi yunkurin kwace wata babbar mota dauke da kayan abinci.

Sanarwar ta ce, “Da ’yan bindigar suka hango jami’an tsaro, sun yi kokarin tserewa. Jami’an tsaron sun bude musu wuta tare da hallaka ’yan bindiga 17, yayin da wasu da dama suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga.”

Jami’an tsaro
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
An Kaddamar Da Ingantattun Shirye-Shiryen Talabijin Da Fina Finan CMG A Bishkek

An Kaddamar Da Ingantattun Shirye-Shiryen Talabijin Da Fina Finan CMG A Bishkek

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.