Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da ƙarin Naira miliyan 148.762 duk wata ga Jami’ar Jihar Gombe (GSU), domin taimakawa wajen biyan ma’aikatan jami’ar alawus ɗin CATA da suke bi.
Za a fara biyan ƙarin tallafin daga Oktoban 2026, wanda zai ƙara yawan tallafin da jami’ar ke samu duk wata da kashi 56 cikin 100.
Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne, ya bayyana hakan ranar Laraba.
Ya ce gwamnan ya kuma bayar da umarnin fara biyan bashin CATA da ma’aikatan jami’ar ke bi.
Wannan mataki ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Manyan Makarantun Jihar Gombe (JOUGTIN) ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14, tare da barazanar shiga yajin aiki kan batutuwan albashi, ƙarin girma da sauran haƙƙoƙin ma’aikata.
Ƙungiyar ta buƙaci aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da ƙarin da ya biyo baya, biyan basussukan albashi, kuɗaɗen ƙarin girma, ƙarin albashi na shekara-shekara da kuma wasu alawus-alawus.
Gwamna Yahaya ya kuma umarci shugabancin jami’ar da ya fara shirye-shiryen biyan sauran basussukan da suka haɗa da bashin ƙarin albashi, mafi ƙarancin albashi da wasu alawus-alawus.
A cewar sakataren, ƙarin kuɗin zai taimaka wa jami’ar wajen tanadar da kuɗin sabon tsarin albashi a cikin ƙarin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026, wanda ake sa ran Majalisar Dokokin Jihar Gombe za ta duba a watan Satumba.
Gwamnati ta ce za a biya sauran basussukan a hankali bisa ƙarfin kuɗin jami’ar, domin kauce wa dakatar da harkokin karatu.
A wani ci gaban kuma, Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta amince da dokar kafa Asusun Tallafa wa Ilimin Jihar Gombe.
Ana sa ran asusun zai samar da ingantaccen tsarin tallafa wa ilimi, musamman Jami’ar Jihar Gombe da sauran manyan makarantun jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma roƙi Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ta yi la’akari da matakan da ake ɗauka wajen magance matsalolin jin daɗin ma’aikata.














