ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
MDD

Majalisar Dattawa ta yi watsi da kiran Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, na a gudanar da bincike karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya (UN) kan sace dalibai da malamai a Karamar Hukumar Oriire ta jihar, tana mai cewa irin wannan bukata na rage muhimmancin wani mummunan lamari da hukumomin tsaron Nijeriya suka samu nasarar warwarewa.

Matsayar ta biyo bayan amincewar Majalisar da wani kuduri na yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Rundunar Sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro bisa nasarar ceto daliban da malamansu bayan sun shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da su.

Kudurin, wanda Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta Tsakiya), ya gabatar tare da goyon bayan dukkan sanatoci, ya kuma karrama jami’an tsaro da suka rasa rayukansu yayin aikin ceton.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da karfafa ayyukan soji da na tattara bayanan sirri wajen yaki da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a fadin kasar.

Kin amincewar Majalisar da ra’ayin Gwamna Makinde ya biyo bayan karin bukatar da Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo ta Arewa) ya gabatar, inda ya nemi a hada da kira ga gwamnan da ya daina neman Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike kan yadda aka yi garkuwa da mutanen da kuma yadda aka kubutar da su.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Sanata Aniekan Bassey (APC, Cross Riber ta Kudu) ne ya mara wa wannan kuduri baya.

A wani jawabi da Gwamna Makinde ya yi wa al’ummar jihar a ranar Litinin, jim kadan bayan sojojin Nijeriya sun mika daliban da malamansu da aka ceto ga gwamnatin jihar, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa masu kare hakkin bil’adama da tabbatar da gaskiya da su binciki yadda lamarin ya faru.

A cewarsa, wannan al’amari ya haifar da tambayoyi da ke bukatar bincike mai zaman kansa wanda ya wuce na hukumomin cikin gida na Nijeriya.

Sai dai Majalisar Dattawa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga aikin ceton, tare da yabawa jami’an tsaron da suka gudanar da aikin saboda kwarewa, jarumtaka da sadaukarwar da suka nuna.

‘Yan majalisar sun yaba wa Babban Hafsan Tsaro, Babban Hafsan Sojojin Kasa, Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Babban Hafsan Sojojin Sama, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) da dukkan jami’ai da dakarun da suka shiga aikin, bisa abin da suka bayyana a matsayin kwarewa ta musamman, kishin kasa da kuma sadaukar da kai wajen yi wa kasa hidima.

A yayin muhawarar, Sanata Adamu Aliero (PDP, Kebbi ta Tsakiya) ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen ceto sauran yaran da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane, musamman a Jihar Borno.

“Har yanzu akwai wasu dalibai da ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane, musamman a Jihar Borno. Ina rokon rundunar sojinmu da ta kara kaimi domin tabbatar da cewa an kubutar da sauran yaran,” in ji shi.

Shi ma Sanata Bictor Umeh (LP, Anambra ta Tsakiya) ya ce nasarar ceton yaran ta dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaron kasar.

“Babu shakka, lokacin da labarin ceton wadannan yara ya bazu, duk ‘yan Nijeriya sun yi matukar farin ciki. Irin wannan labari ne muke son ci gaba da ji. Abin da muka dauka ba zai yiwu ba, yanzu ya zama abin da aka iya yi. Na yi matukar farin ciki da wannan aiki,” in ji shi.

Haka kuma, Sanata Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa) ya bukaci rundunar soji da ta nuna irin wannan gaggawa wajen ceto sauran yaran da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane a wasu sassan Jihar Borno.

“Muna da irin wadannan sace-sacen mutane. A jihata, musamman a mazabar Sanata Ndume, har yanzu akwai yara da ke tsare. Ina rokon rundunar soji ta nuna irin wannan gaggawa domin a kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane,” in ji shi.

Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya) ya roki Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, da ya ci gaba da karfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro kuma ya taimaka wajen samun nasarar aikin ceton, tare da amfani da irin wannan tsari a sauran ayyukan tsaro a fadin kasar.

MDD
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Kura-kurai 7 Da Mata Ke Yi Wajen Kula Da Fatarsu

Kura-kurai 7 Da Mata Ke Yi Wajen Kula Da Fatarsu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.