Tsawon shekaru., Kudancin Kaduna an fi saninsa da harkar gona, matsalolin tsaro da ke yawan faruwa, da kuma wuraren shakatawa na bude ido da ba a amfana da su ba. Amma a karkashin duwatsunta da kauraran gonakanta, akwai wani boyayyen labarin da yanzu haka ya fara sauya alkiblar tattaunawa kan makomar tattalin arzikin Nijeriya.
Nijeriya tana da kimanin Dalar Amurka biliyan 750 na arzikin ma’adanai da ba a hako ba da ke bazuwa a wurare masu muhimmanci 44. A nan gida, wadannan albarkatu, da suka hada da sinadarin lithium, zinari, tama (iron ore), da bami (bitumen), suna samar da babbar dama ta karkata akalar tattalin arziki daga dogaro da mai kadai, sannan su samar da gagarumar hanyar samun kudin shiga ga al’ummomin yankin.
Tabbatarwar da gwamnatin tarayya ta yi cewa Jihar Kaduna tana kunshe da wani babban yanki mai arzikin ma’adanai daban-daban na duniya wanda ya hada da tagulla (platinum group metals), lithium, nickel, zinari, jan karfe (copper), da wasu sinadaran kasa (rare earth elements), ya sake maida hankalin kasa da na duniya baki daya zuwa ga Kudancin Kaduna.
Yayin da wannan sanarwa ta zo a matsayin labarin dumi-dumi a birnin Abuja, shi kuwa asalin labarin ya dade da farawa a hankali watanni da dama da suka gabata a wasu kauyuka masu nisa da suka hada iyaka da masarautar Kaninkon a Karamar Hukumar Jema’a da masarautar Kagoro a Karamar Hukumar Kaura, inda aka dade ana tsananin hakar lithium ba tare da sanarwar jama’a ba.
Hanyar hakar ma’adanai mai tsauraran tsaro
Lalacewar hanyar da ta kai ga inda ake hakar ma’adanan ba ta bayyana ainihin abin da ke can gaba ba.
Bayan tafiyar kilomitoci da dama a cikin sarkakkiyar daji da duwatsu, sai tafiyar ta fara yin wahala da takurawa, domin an amincewa ma’aikata na musamman kadai su shiga inda ake hakar ma’adanan.
Jaridar Weekend Trust ta ruwaito cewa jami’an hukumar tsaron fararen hula ta kasa (NSCDC) da na rundunar tsaron sa-kai ta Jihar Kaduna (KADBS) ne ke kula da zirga-zirga a yankin. Daya daga cikinsu da ya zanta da wakilinmu ya yi bayanin cewa ma’aikata, dillalan ma’adanai masu lasisi, jami’an kamfani, da kuma mutanen da ke da takardar izini na musamman ne kadai aka amince musu su shiga yankin da ake aikin.
“Wannan wuri ne da aka takaita shiga cikinsa. Kana bukatar amincewa kafin ka shiga,” in ji wani jami’in tsaro da yake tattaunawa da wakilinmu.
Wannan tsauraran matakan tsaro a wurin hakar ma’adanan yana nuna muhimmancin da aka dorawa sinadarin lithium, ma’adanin da a halin yanzu ake daukarsa a matsayin “farar zinariya” a fadin duniya saboda rawar da yake takawa wajen kera batirirrikan motocin zamani na lantarki (electric behicles), na’urorin adana makamashi na rana, da kuma kayayyakin lantarki na zamani.
Shekara guda ta harkokin kasuwanci.
Ko da yake ba masu mallakar kasar ko wakilan daya daga cikin kamfanonin hakar ma’adanan suka amince su bayyana cikakkun bayanai game da yadda ake gudanar da aikin hakar ma’adanai a yankin ba, bincike ya nuna cewa ana gudanar da harkokin hakar ma’adanai na kasuwanci kusan shekara guda kenan. Haka kuma, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin masu mallakar kasar da kamfanonin da ke gudanar da aikin kan batutuwa daban-daban da suka shafi amfani da kasa da kuma biyan diyya.
An lura cewa kamfanonin suna gudanar da aikin hakar ma’adanai daga ranar Litinin zuwa Alhamis, yayin da ranakun Juma’a da Asabar ake ware su domin masu mallakar kasar.
Kokarin da Weekend Trust ta yi na samun bayanin hukuma daga wakilan kamfanonin bai haifar da wani gamsasshen sakamako ba. Haka kuma, masu ruwa da tsaki daga al’ummomin yankin sun ki yin magana, suna masu cewa akwai yarjejeniyoyin sirri da suka hana su bayyana bayanai. Sai dai kasancewar manyan injinan hakar ma’adanai, jami’an tsaro da kuma ci gaba da zirga-zirgar manyan motoci na nuna babu shakka ana gudanar da babban aikin hakar ma’adanai a yankin.
Mazauna yankin sun ce baya ga ma’adanin lithium, binciken farko ya kuma nuna akwai ma’adanin konzalite da wasu ma’adanai masu alakar da shi. Sai dai har yanzu ana jiran tabbacin hukuma kan wannan bayani.
Ko da yake har yanzu ana ci gaba da tsaurara matakan kula da shiga wurin hakar ma’adanan, Weekend Trust ta tattaro bayanai daga wani ma’aikaci da ya saba da yadda ake gudanar da aikin, wanda ya ce yawan aikin hakar ma’adanan ya karu matuka cikin shekara guda da ta gabata. Ya bayyana cewa kowace babbar mota da ke barin wurin tana dauke da kimanin tan 40 na dutsen lithium, yayin da a ranakun da ake gudanar da cikakken aiki ake fitar da manyan motoci sama da 10 daga wurin.
Mazauna yankin sun nuna fata, tare da yin taka-tsantsan
Baya ga farin cikin da aka samu sakamakon gano sabbin ma’adanan, mazauna yankin sun shaida wa Weekend Trust cewa abin da ya fi muhimmanci a gare su shi ne yadda arzikin ma’adanan zai inganta rayuwarsu ta yau da kullum.
Wani mazaunin masarautar Kaninkon, John Tonah Daniel, ya shaida wa wakilinmu cewa ayyukan hakar ma’adanai a yankin sun jawo hankalin al’ummomin da ke kewaye. Sai dai ya ce mutane da dama ba su san girman aikin ba saboda tsauraran matakan tsaro da aka kafa a wurin.
Ya ce, “Mutane sun san cewa ana gudanar da wani babban aiki saboda yawan zirga-zirgar manyan motoci da kuma tsauraran matakan tsaro, amma an hana jama’a shiga wurin. Saboda haka, yawancin mazauna yankin bayanan da suke samu daga ma’aikata ne ko kuma mutanen da aka ba izinin shiga. Muna fatan wannan aiki zai samar wa matasanmu guraben aikin yi tare da inganta al’ummominmu.”
Daniel ya bukaci gwamnati da kamfanonin hakar ma’adanai su ci gaba da tattaunawa akai-akai da al’ummomin da aikin ya shafa domin kauce wa samun rashin fahimtar juna.
Ya kara da cewa, “Bai kamata kamfanoni kadai su amfana da hakar ma’adanan ba. Al’ummomin da aka gano wadannan ma’adanai a cikinsu su ma ya kamata su ci moriya ta hanyar samun ingantattun hanyoyi, makarantu, cibiyoyin lafiya da kuma guraben aikin yi.”
Wani mazaunin yankin, Tanko Gworok, ya ce mutane da dama sun yi maraba da tabbacin da gwamnatin tarayya ta bayar game da gano wadannan ma’adanai, yana mai cewa hakan ya kara tabbatar da cewa Kudancin Kaduna na da dimbin arzikin ma’adanai da har yanzu ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba.
Ya ce, “Wannan sanarwa ta sake farfado da fatan al’ummarmu. Tun da dadewa mun yi imanin cewa kasarmu na dauke da ma’adanai masu matukar daraja. Abin da muke so yanzu shi ne a gudanar da hakar ma’adanan cikin gaskiya da kulawa da muhalli, tare da samar da damammaki ga mutanen yankin.”
A cewarsa, mazauna yankin na kuma sa ran a gudanar da tsarin biyan diyya ga masu mallakar kasa cikin gaskiya da bayyana komai a fili.
Ya ce, “Ya kamata gwamnati ta tabbatar an mutunta duk wata yarjejeniya tsakanin kamfanonin hakar ma’adanai da al’ummomin da aikin ya shafa. Ya kamata ci gaba ya tafi tare da ayyukan hakar ma’adanai domin al’ummomi masu zuwa su tuna wannan lokaci a matsayin farkon kyakkyawan sauyi.”
Ayyukan da ake gudanarwa cikin natsuwa a Kudancin Kaduna sun samu cikakken tabbaci a matakin kasa lokacin da Ministan Raya Ma’adanai, Dele Alake, ya sanar da gano abin da ya bayyana a matsayin daya daga cikin manyan yankunan ma’adanai masu nau’o’i daban-daban mafi muhimmanci a nahiyar Afirka.
Da yake jawabi a taron Taron Zuba Jari kan Albarkatun kasa da Makamashi na Afirka. (AFNIS) 2026 da aka gudanar a Abuja, Alake ya bayyana cewa binciken da wani kamfani mai zaman kansa ya gudanar, wanda kuma Hukumar Binciken Kasa da Ma’adanai ta Nijeriya ta tabbatar, ya gano ma’adanai masu matukar amfani ga harkokin kasuwanci da suka hada da Ma’adanan rukunin platinum, lithium, nickel da tagulla (copper), gold da kuma rare earth elements.
A cewar ministan, wannan bincike ya sanya Nijeriya cikin jerin kasashen da ke zama sabbin cibiyoyin samar da muhimman ma’adanan da ake bukrata wajen fasahohin makamashi mai tsafta da kuma masana’antun zamani.
Alake ya ce, “Wannan ne karon farko da nake bayyana wannan bayani a bainar jama’a,” yana mai bayyana wannan nasara a matsayin wani babban ci gaba a shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunkasa tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun kudaden shiga.
Ba tun yau labarin arzikin ma’adanan Kudancin Kaduna ya fara ba.”
Sai dai ga mazauna Karamar Hukumar Jema’a, sanarwar da aka yi a baya-bayan nan wani sabon babi ne kawai a tarihin arzikin ma’adanan yankin, wanda ya fara kusan shekara goma da suka gabata.
A shekarar 2016, masana ilimin kasa (geologists) sun sanar da gano daya daga cikin ma’adanan nickel mafi inganci a duniya a garin Dangoma, da ke masarautar Kaninkon. Wannan bincike ya jawo hankalin al’umma a fadin kasar.
Jami’an gwamnati, masu zuba jari daga kasashen waje da kwararrun masana hakar ma’adanai sun kai ziyara yankin, yayin da mazauna suka yi tsammanin za a samu sauyi cikin sauri ta fuskar hanyoyi, makarantu, samar da ayyukan yi da kuma inganta harkokin lafiya.
Tsohon Ministan Raya Ma’adanai, Dakta Kayode Fayemi, ya taba bayyana cewa amfani da dimbin arzikin ma’adanan Nijeriya yadda ya kamata na iya kara kimanin Dala biliyan 25 ga jimillar darajar tattalin arzikin kasar (GDP).
Nan da nan Dangoma ta zama daya daga cikin wuraren hakar ma’adanai da aka fi magana a kansu a Nijeriya.
Babban fata, amma ci gaba ya yi tafiyar hawainiya
Shekara goma bayan wannan gagarumin bincike, mazauna yankin sun ce sauye-sauyen da suke tsammani ba su zo cikin saurin da aka yi fata ba.
Weekend Trust ta ruwaito cewa, duk da cewa an ci gaba da gudanar da binciken ma’adanai a matakai daban-daban a Dangoma, Bakin Kogi da sauran al’ummomin da ke makwabtaka, har yanzu manyan ayyukan more rayuwa ba su kai matsayin da al’ummar yankin suke fata ba.
Shugabannin al’umma sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da kamfanonin hakar ma’adanai, wadanda suka hada da biyan diyya ga manoman da ayyukan suka shafa, gyaran muhalli bayan an gama hakar ma’adanai, gina azuzuwan karatu, hakar rijiyoyin burtsatse, biyan kudin jarabawa ga dalibai da kuma ba matasan yankin da suka cancanta fifiko wajen samun aikin yi. Sai dai mazauna yankin sun ce har yanzu ba a cika wasu daga cikin wadannan alkawuran gaba daya ba.
Tsohon hakimin Dangoma ya taba rokron gwamnati da ta samar da karin makarantu, ta inganta ayyukan kiwon lafiya, tare da gina hanyar Dangoma zuwa Godogodo domin tallafa wa harkokin noma da kuma hakar ma’adanai.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu wadannan bukatu na nan daram kuma suna da muhimmanci ga al’ummar yankin.
Damammaki da suka wuce hakar ma’adanai.
Masana sun bayyana cewa muhimmancin wannan sabon yankin da aka tabbatar yana dauke da dimbin ma’adanai bai takaitu ga fitar da danyen ma’adanai zuwa kasashen waje kawai ba. Ma’adanin lithium ya zama daya daga cikin muhimman ma’adanai da ake matukar bukrata a duniya saboda karuwar amfani da batura masu caji da ake amfani da su a motocin lantarki, wayoyin salula da kuma tsarin adana makamashi daga hanyoyin samar da makamashi mai sabuntawa.
Haka kuma, nickel na da matukar muhimmanci wajen samar da krarfen stainless steel, fasahar sararin samaniya, kera batir da kuma masana’antu daban-daban.
Weekend Trust ta kuma ruwaito cewa ma’adanan platinum group metals suna da matukar amfani wajen kera na’urorin rage gurbata hayaki a motoci (catalytic conberters), fasahar makamashin hydrogen, na’urorin lantarki da kuma kayan ado. Haka nan, rare earth elements suna taimakawa wajen kera maganadisu, injinan samar da wutar iska (wind turbines), kayan aikin tsaro da kuma fasahohin sadarwa na zamani.
Masana na ganin cewa idan aka gudanar da wannan arzikin ma’adanai yadda ya kamata, Jihar Kaduna na iya zama daya daga cikin manyan wuraren da masu zuba jari za su fi mayar da hankali a fannin hakar ma’adanai a Nijeriya.
Gwamnatin tarayya ta ce darussan da aka koya daga abubuwan da suka faru a baya a fannin hakar ma’adanai ne suka sa aka dauki wata sabuwar hanya wajen tafiyar da harkar. A cewar Ministan Raya Ma’adanai, Dele Alake, tuni an soke lasisin hakar ma’adanai sama da 3,000 da ba sa aiki domin kara tabbatar da gaskiya da rike hakrkrin hakar ma’adanai ga masu zuba jari na gaske kadai.
Haka kuma, sabuwar manufar gwamnati ta tanadi cewa duk mai neman lasisin hakar ma’adanai dole ne ya gabatar da shirin sarrafa ma’adanan a cikin gida, maimakon fitar da su a matsayin danyen kaya.
Sauye-sauyen da aka aiwatar sun riga sun jawo zuba jarin biliyoyin Daloli a masana’antun sarrafa lithium da sauran ayyukan tace ma’adanai a sassa daban-daban na Nijeriya. Alkaluman hukuma sun nuna cewa kudaden shiga da gwamnatin ke samu daga fannin hakar ma’adanai sun karu daga Naira biliyan 6 kafin gwamnatin da ke kan mulki ta hau karagar mulki zuwa sama da Naira biliyan 70 a karshen shekarar 2025.
Al’ummomin da ke daukar nauyin ayyukan hakar ma’adanai na sa ido sosai
Weekend Trust ta ruwaito cewa a Kudancin Kaduna, farin cikin da aka samu ya hadu da taka-tsantsan da kuma kyakkyawan fata, yayin da mazauna da dama ke fatan sabon hankalin da kasa ta mayar kan yankin zai haifar da ci gaba da za a gani a zahiri.
Abubuwan da suke fata sun hada da ingantattun hanyoyi, makarantu mafi kyau, cibiyoyin kiwon lafiya, tsaftataccen ruwan sha, damar samun ayyukan yi da kuma karin matakan kare muhalli. Wasu kuma na fatan gwamnati za ta tabbatar an aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin kamfanonin hakar ma’adanai da al’ummomin da aikin ya shafa gaba daya.
Shugabannin gargajiya da kungiyoyin matasa sun kuma ce zaman lafiya da fahimtar juna na da matukar muhimmanci idan al’ummomi za su amfana sosai daga bunkasar hakar ma’adanai.
Wakilinmu ya kuma lura cewa, duba da abubuwan da ke faruwa a kewayen wurin hakar ma’adanan, tsaro na ci gaba da kasancewa babban abin damuwa. Tsauraran matakan tsaro da aka kafa a wurin hakar lithium sun kuma nuna wata gaskiya mai muhimmanci.
Haka kuma, muhimman ma’adanai na dabarun tattalin arziki suna kara zama masu matukar daraja a duniya, lamarin da ke sa wuraren hakar ma’adanai su zama abin hari ga masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma kungiyoyin masu aikata laifuka.
Saboda haka, hukumomin tsaro na fuskantar nauyi biyu: kare kadarorin tattalin arzikin kasa tare da ci gaba da kyautata dangantaka da al’ummomin da ke daukar nauyin ayyukan hakar ma’adanai.
Yayin da mazauna al’ummomin da ake hakar ma’adanai ke ci gaba da fatan cewa wata rana arzikin da ke karkashin kasarsu zai inganta rayuwarsu, amsar tambayar ita ce, ko wannan boyayyen arziki zai zama albarka ko kuma wata dama da za ta kubuce za ta dogara ne kan ingantaccen tsari da sa ido, kare muhalli, bai wa al’umma damar shiga cikin al’amura, gaskiya da rikon amana, da kuma ci gaba da zuba jari.
Sabon man fetur
Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan irin gagarumin tasirin tattalin arzikin da ma’adanin lithium zai iya yi wa al’ummomin da abin ya shafa kai tsaye da kuma kasar baki daya, masana sun bukaci gwamnati ta bai wa sarrafa lithium a cikin gida da kara masa kima fifiko maimakon fitar da danyen ma’adanin zuwa kasashen waje. Sun ce gina cikakkiyar sarrafawar lithium daga farko har karshe zai samar da ayyukan yi, ya jawo masu zuba jari, ya bunkasa masana’antu tare da taimakawa wajen fadada tattalin arzikin kasar fiye da dogaro da danyen man fetur.
Masanan sun bayyana hakan ne yayin da suke bayani kan irin damar tattalin arzikin da ke tattare da karin gano ma’adanan lithium a Nijeriya, inda suka jaddada cewa babbar ribar da kasar za ta samu ita ce idan ta sarrafa ma’adanin zuwa sinadaran lithium da ake amfani da su wajen kera batir masu inganci, tare da bunkasa masana’antun da ke amfani da wadannan kayayyaki.
Da yake zantawa da Weekend Trust a ranar Alhamis, wani malami kuma mai bincike a Sashen Kimiyyar Kasa (Department of Geosciences) na Jami’ar Legas, Dakta Daniel Obasaju, ya bayyana lithium a matsayin daya daga cikin muhimman ma’adanai na dabarun tattalin arziki a duniya saboda muhimmiyar rawar da yake takawa wajen kera batira masu caji da ake amfani da su a motocin lantarki, tsarin adana makamashi daga hanyoyin makamashi mai sabuntawa, na’urorin lantarki na masu amfani, fasahar sararin samaniya da sauran masana’antun fasaha na zamani.
A cewarsa, arzikin lithium da Nijeriya ke da shi na ba kasar babbar dama ta bunkasa tattalin arzikinta, kara wa gwamnati kudaden shiga da kuma jawo zuba jarin kasashen waje kai tsaye.
Ya ce, “Sai dai babbar ribar tattalin arziki ba ta ta’allaka ne ga fitar da danyen ma’adanin lithium zuwa kasashen waje ba, illa ta hanyar gina cikakkiyar kimar da ta hada da inganta ma’adanin, samar da sinadaran lithium masu ingancin kera batir, kera batir da kuma bunkasa sauran masana’antun da ke dogaro da wadannan kayayyaki.”
Ya bayyana cewa Nijeriya ta riga ta fara tafiya a kan hanya mai kyau ta hanyar karfafa sarrafa ma’adanin lithium a cikin gida.
Obasaju ya yi nuni da kaddamar da masana’antar sarrafa lithium mafi girma a Yammacin Afirka da ke Jihar Nasarawa, wadda Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar kwanan nan, a matsayin wani muhimmin ci gaba a kokarin kasar na kara wa ma’adananta kima.
A cewarsa, masana’antar na da karfin sarrafa kimanin tan 6,000 na danyen ma’adanin lithium a kowace rana, tare da hasashen iya sarrafa kusan tan miliyan uku a duk shekara.
Ya kara da cewa masana’antar ta riga ta samar da ayyukan yi kai tsaye sama da 1,000, sannan ta samar da fiye da guraben aiki 2,000 a kaikaice.
Ya ce, “Wannan na nuna cewa Nijeriya ta fara sauya salo daga fitar da danyen ma’adanai zuwa sarrafa su a cikin gida. Hakan zai samar da ayyukan yi, ya bunkasa masana’antu, ya saukaka musayar fasaha tare da taimaka wa kasar ta rike mafi yawan ribar tattalin arzikin da ma’adanan ke samarwa.”
Obasaju ya bukaci gwamnati ta ci gaba da karfafa manufofin da za su tabbatar Nijeriya ta amfana da albarkatun kasarta ta hanyar bunkasa masana’antu a cikin gida maimakon dogaro da fitar da danyen ma’adanai.
Hakazalika, wani masanin ilimin kasa mai amfani (Applied Geologist), Oyelana Elijah, ya ce ma’adanan lithium da ake da su a jihohin Nasarawa, Kaduna, Ekiti da Kogi na iya zama babban tushen bunkasar tattalin arzikin kasa idan aka kara sarrafa su a cikin gida.
Ya ce bunkasa harkar lithium za ta samar da ayyukan yi a dukkan sassan haka da sarrafa ma’adanan, ta samar da wata hanyar samun kudaden shiga da ba ta dogara da danyen man fetur ba, tare da jawo masu zuba jari daga kasashen waje zuwa fannonin masana’antu da makamashi mai tsafta.
A cewar Elijah, lithium wani muhimmin sinadari ne wajen kera batir na motocin lantarki da kuma tsarin adana makamashi daga hanyoyin makamashi mai sabuntawa, lamarin da ya sa darajarsa ke ci gaba da karuwa yayin da duniya ke komawa amfani da makamashi mai tsafta.
Ya ce, “Lithium na iya taimakawa wajen samar da ayyukan yi, jawo masu zuba jari daga kasashen waje, inganta tsarin adana makamashi, bunkasa masana’antu da kuma samar wa kasar wata hanyar samun kudaden musayar kasashen waje.”
Sai dai Elijah ya yi gargadin cewa Nijeriya na fuskantar hadarin rasa babban bangare na ribar tattalin arzikin wannan ma’adini idan ta ci gaba da fitar da danyen lithium zuwa kasashen waje maimakon sarrafa shi a cikin gida.
Ya ce, “Muna fitar da lithium zuwa kasashen waje, amma idan za mu iya sarrafa shi a Nijeriya, hakan zai fi amfani a gare mu. Sai idan muka sarrafa shi a cikin gida ne za mu samu cikakkiyar ribar tattalin arzikin da wannan albarkatu ke tattare da ita.”
A cikin ‘yan shekarun nan, Nijeriya ta jawo karin zuba jari a fannin hakar da sarrafa lithium, yayin da bukatar ma’adanan da ake amfani da su wajen kera batir ke ci gaba da karuwa a duniya, sakamakon bunkasar motocin lantarki da fasahohin makamashi mai sabuntawa.
Masanan sun jaddada cewa karfafa karfin sarrafa ma’adanai a cikin gida da bunkasa masana’antun da ke amfani da su bayan sarrafawa zai ba Nijeriya damar samun karin riba daga albarkatun ma’adananta, tare da samar da ayyukan yi da kuma tallafa wa ci gaban masana’antu na dogon lokaci.













