Kwamitin kolin JKS ya kira taron karawa juna sani tare da wadanda ba ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ba, da nufin sauraron ra’ayoyi, da shawarwari dangane da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma yadda aikin raya tattalin arzikin kasar ke gudana a watanni shida na karshen shekarar nan ta 2026.Sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ne ya jagoranci taron na ranar 24 ga watan nan, tare da gabatar da muhimmin jawabi.
A jawabinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, domin gudanar da managarcin aiki a fannin raya tattalin arziki, a tsagi na biyu na shekarar nan, ya zama wajibi a nacewa babbar ka’idar neman ci gaba yayin da ake wanzar da daidaito, da aiwatar da cikakken sabon tsarin neman ci gaba, kana a gaggauta gina sabon salon bunkasa kasa, da kyautata tsare-tsaren yanayi daban daban da ake fuskanta a gida da matakin kasa da kasa.
Shugaba Xi, ya ce wajabi ne a nacewa zurfafa sauye-sauye da bude kofa, da ingiza ginshikan samar da ci gaba tsaffi da sababbi, da fadada kokarin bunkasa bukatun gida, da inganta samar da hajoji, ta tabbatar da matakan kyautata rayuwar al’ummar kasa, da inganta karsashin samar da ci gaba, da bunkasa zamantakewar jama’a, da ingiza tattalin arziki ta yadda za a samar da sabuwar alkibla, da turba ta gari, da kara kaimin bude ayyukan raya kasa karkashin manufar raya kasa ta shekaru biyar-biyar karo na 15. (Saminu Alhassan)














