Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnoni su daina gina gadar sama a wuraren da babu cunkoson ababen hawa, maimakon haka su mayar da hankali wajen gina hanyoyin da za su inganta rayuwar al’umma tare da sauƙaƙa wa jami’an tsaro isa yankunan karkara.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya karɓi bakuncin sarakunan gargajiya daga Jihar Oyo.
Ya ce jihohi na samun kuɗi sau huɗu zuwa sau biyar fiye da yadda suke samu a baya daga Asusun Gwamnatin Tarayya, don haka ya kamata su yi amfani da kuɗin wajen aiwatar da ayyukan da za su amfani jama’a.
Shugaban ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ‘yan ta’adda ko biyan kuɗin fansa domin ceto waɗanda aka sace ba.
Ya ce waɗanda suka sace ɗaliban makarantar da aka ceto a Jihar Oyo sun buƙaci a sako wasu daga cikin ‘yan ƙungiyarsu da ke tsare, amma gwamnati ta yi watsi da buƙatar.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnati na faɗaɗa rundunar sojoji daga rundunoni takwas zuwa 12 domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da kuma inganta saurin kai ɗauki wajen magance matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.














