Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya zaɓi Shugaban Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Jihar Kaduna (KADIRS), Jerry Adams, a matsayin abokin takararsa a zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kuma hakan na nuna ƙudirinsa na tabbatar da adalci, haɗin kai da shugabanci na gari.
Ya bayyana Adams a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati wanda ya taimaka wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga na jihar ta hanyar gaskiya da sabbin dabaru.
Uba Sani ya buƙaci al’ummar Kaduna su goyi bayan wannan zaɓi tare da fifita haɗin kai da ci gaban jihar, maimakon bambancin addini ko ƙabilanci.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su ƙarfafa zaman lafiya da ci gaba.














