Jam’iyyar APC reshen Jihar Delta ta musanta rahotannin da ke cewa an samu tashin hankali a taron masu ruwa da tsaki da ta gudanar a Effurun.
Jam’iyyar ta ce an gudanar da taron cikin lumana kuma ya ƙare ba tare da wata matsala ba.
Ta ƙara da cewa an watsa taron kai-tsaye a talabijin, wanda ya bai wa kowa damar tabbatar da yadda aka gudanar da shi.
APC ta kuma yi watsi da wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, tana mai cewa an ɗauke shi ne a wani waje dabam a harabar cibiyar PTI.
Jam’iyyar ta bai wa wata jarida wa’adin kwanaki bakwai da ta janye rahoton tare da neman afuwarta.
Ta ce idan hakan bai faru ba, za ta ɗauki matakin shari’a.
Har ila yau, APC ta musanta zarge-zargen da ke cewa akwai rikicin shugabanci a jihar, tana mai cewa shugabanninta an zaɓe su bisa ƙa’ida kuma jam’iyyar ta ƙasa ta amince da su.














