ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 29, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Dangote Na Kara Karfafa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Jihar Neja

by Bello Hamza
1 month ago
Dangote

Kamfanin Dangote Industries Limited (DIL) na hada gwiwa da gwamnatin Jihar Neja domin hanzarta bunkasa masana’antu, bude hanyoyin saka hannun jari, da kuma samar da dorewar arziki a jihar, sakamakon kudurin kamfanin na tallafa wa ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.

Wata sanarwa daga Babban Jami’in Hulda da Jama’a da Sadarwa na rukunin kamfanin, Anthony Chiejina, ce ta bayyana cewa a halin yanzu kamfanin na aiki tare da gwamnatin jihar domin fadada damar tattalin arziki a jihar.

Mai magana da yawun ya ce baya ga daukar nauyin bikin baje kolin kasuwanci na shekara-shekara, kamfanin Dangote Rice Limited ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da gwamnatin jihar kan samar da shinkafar paddy cikin shekaru 10 masu zuwa.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta kara da cewa: “Bisa ga yarjejeniyar, Dangote Rice Limited ya yi alkawarin sayen tan miliyan 1 na shinkafar paddy, wanda kamfanin Niger Foods zai samar domin kara wadatar abinci a Nijeriya.”

Sanarwar ta ambato Daraktar Yanki kuma Babbar Mai Bai wa Shugaban Kamfanin Dangote Group shawara, Fatima Wali-Abdurrahman, tana cewa aikin gina matatar shinkafar kamfanin a jihar na ci gaba yadda ya kamata.

LABARAI MASU NASABA

Shigo Da Fetur Daga Waje Ya Sauka Zuwa N983.92, Ya Fi Na Matatar Dangote Arha

An Lakaɗawa Wata Malamar Makaranta Duka Har Lahira A Lokoja

Ta ce: “Aikin gina matatar shinkafar Dangote mai karfin sarrafa tan 32 a cikin awa guda (MTPH), wadda ake ginawa a filin hekta 30 da ke Wushishi, na tafiya yadda ya kamata kuma ana sa ran kammala ta cikin lokaci. Wannan babban aiki wata muhimmiyar nasara ce wajen karfafa shirye-shiryen samar da wadatar abinci a jihar. Bayan an kammala aikin, ana sa ran matatar za ta kara yawan noman shinkafa a gida, samar da guraben ayyukan yi, tare da taimakawa ci gaban harkokin noma a Nijeriya.”

Haka kuma, Misis Wali-Abdurrahman ta ce sassan kasuwancin kamfanin suna halartar bikin baje kolin kasuwanci na Jihar Neja karo na 22.

Kamfanin Dangote shi ne babban mai daukar nauyin bikin baje kolin kasuwanci na kasa na Jihar Neja wanda za a bude a hukumance ranar Alhamis, 14 ga Mayu, 2026, kuma taken bikin shi ne: “Hadin Gwiwar Gwamnati da Kamfanoni Masu Zaman Kansu a Matsayin Mafita ga Ci gaban da Daidaiton Tattalin Arzikin Nijeriya.”

Ta bayyana cewa sassan kamfanin da ke halartar bikin sun hada da Dangote Cement Plc, Dangote Salt (NASCON), Dangote Sugar Refinery (DSR), Dangote Fertiliser Limited (DFL), da sauransu.

Ta kara da cewa akwai teburi na musamman domin taimaka wa mahalarta wajen samun bayanai kan Dangote Refinery, hangen nesa na kamfanin zuwa shekarar 2030, da sauran harkokin kasuwancinsa.

Da yake zantawa da manema labarai a Minna, Babban Daraktan Kungiyar Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Jihar Neja (NCCIMA), Adamu Salihu, ya ce ana sa ran bikin baje kolin na bana zai jawo mahalarta kusan 300, ciki har da masu zuba jari, masu tsara manufofi, da shugabannin kasuwanci daga sassa daban-daban na kasar nan.

Malam Salihu ya ce: “Dangote ba wai yana bunkasa masana’antu a Nijeriya kadai ba ne, har ma a duk fadin Afirka. Kungiyar Kasuwanci ta Jihar Neja za ta yi amfani da bikin baje kolin wajen nuna nasarorin Dangote ga al’ummar jihar, Nijeriya da ma Afirka baki daya.”

Ya kara da cewa: “Kasancewar Dangote Group na ci gaba da halartar bikin baje kolin kasuwanci na Jihar Neja a kowace shekara na daga cikin manyan dalilan da ke karfafa Kungiyar Kasuwanci ta jihar wajen shirya bikin duk shekara.

“Daya daga cikin muhimman darussan da ‘yan kasuwar Nijeriya za su koya daga jarumtakar hangen nesan zuba jari na Dangote shi ne bukatar yarda da Nijeriya da kuma saka hannun jari a cikin dimbin damarmakin da kasar ke da su. Gina Nijeriya irin wadda muke mafarki na bukatar kamfanonin cikin gida su jagoranci bunkasa masana’antu da ci gaban tattalin arziki.

“Ko da yake masu zuba jari daga kasashen waje na taka muhimmiyar rawa, babban manufarsu ita ce samun ribar da daga karshe za su mayar zuwa kasashensu. Amma zuba jari na cikin gida yana samar da dorewar amfani ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa kwarewa, da samar da arzikin kasa mai dorewa.”

Shugaban Niger Foods, Sammy Adigun, ya ce Jihar Neja na bukatar bunkasa hekta 25,000 na gonakin shinkafa na kasuwanci, ya kara da cewa hadin gwiwar zai dauki shekaru 10 kuma zai samar da ayyukan yi kai tsaye har 50,000.

Dangote
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jagoran Matasan AAC Kwamret Yahaya Soje Ya Nemi A Saki Sowore
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar NPCF Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Ga Tinubu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Hijira 1448:Za A Samu Yalwar Tattalin Arziƙi A Nijeriya —Sheikh Muhajjadina

MASU ALAKA

Shigo Da Fetur Daga Waje Ya Sauka Zuwa N983.92, Ya Fi Na Matatar Dangote Arha
Manyan Labarai

Shigo Da Fetur Daga Waje Ya Sauka Zuwa N983.92, Ya Fi Na Matatar Dangote Arha

June 28, 2026
An Lakaɗawa Wata Malamar Makaranta Duka Har Lahira A Lokoja
Manyan Labarai

An Lakaɗawa Wata Malamar Makaranta Duka Har Lahira A Lokoja

June 28, 2026
Ƴan Bindiga Sun Harbe Limami Da Wasu Mutane 3 A Sokoto
Labarai

Ƴan Bindiga Sun Harbe Limami Da Wasu Mutane 3 A Sokoto

June 28, 2026
Next Post
Iran Ta Jinjinawa Kasar Sin

Iran Ta Jinjinawa Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Ana Taron Ministocin Kula Da Yawon Bude Ido Na Kasashen APEC A Macao

Ana Taron Ministocin Kula Da Yawon Bude Ido Na Kasashen APEC A Macao

June 28, 2026
Shigo Da Fetur Daga Waje Ya Sauka Zuwa N983.92, Ya Fi Na Matatar Dangote Arha

Shigo Da Fetur Daga Waje Ya Sauka Zuwa N983.92, Ya Fi Na Matatar Dangote Arha

June 28, 2026
An Lakaɗawa Wata Malamar Makaranta Duka Har Lahira A Lokoja

An Lakaɗawa Wata Malamar Makaranta Duka Har Lahira A Lokoja

June 28, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Gaggauta Zamanantar Da Tsarin Ayyukan Masana’antu

Mataimakin Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Gaggauta Zamanantar Da Tsarin Ayyukan Masana’antu

June 28, 2026
Kotu Ta Fara Sauraron Shari’ar Da Ke Ƙalubalantar Takarar Pantami A PDP

Kotu Ta Fara Sauraron Shari’ar Da Ke Ƙalubalantar Takarar Pantami A PDP

June 28, 2026
Ƴan Bindiga Sun Harbe Limami Da Wasu Mutane 3 A Sokoto

Ƴan Bindiga Sun Harbe Limami Da Wasu Mutane 3 A Sokoto

June 28, 2026
Ƴansanda Sun Kama Mutum 10 Kan Kisan Shugaban MACBAN Na Jihar Binuwe

Ƴansanda Sun Kama Mutum 10 Kan Kisan Shugaban MACBAN Na Jihar Binuwe

June 28, 2026
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Ziyarci Iyalan Malamar Addini Da Aka Kashe A Kaduna Saboda Zargin Satar Yara

June 28, 2026
Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Yadda Aka Hallaka Malamar Islamiyya A Kaduna

Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Yadda Aka Hallaka Malamar Islamiyya A Kaduna

June 28, 2026
Abubuwan Da Ke Tattare Da Jami’in Soja Sambo Dasuki

Abubuwan Da Ke Tattare Da Jami’in Soja Sambo Dasuki

June 28, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.