ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hijira 1448:Za A Samu Yalwar Tattalin Arziƙi A Nijeriya —Sheikh Muhajjadina

by Bello Hamza and Sulaiman
3 months ago
Tattalin arziki

A yayin da al’ummar musulmin duniya ke murnar shiga sabuwar shekarar musulu7nsi ta Hijira 1448, an yi hasashen cewa, duk da ƙasasshen duniya za su fuskanci matsin tattalin arziƙi amma za a samu yalwa da ƙaruwar tattalin arzƙi a tsakanin talakawan Nijeriya. Wannan hasashen ya fito ne daga bakin Sheikh Muhajjadina Sani Kano Alfalaki wanda kuma shi ne shugaban masu ilimin taurari na nahiyar Afrika gaba ɗaya a tattaunawarsa da Wakilijmu ta wayar tarho daga birnin Makka.

Bayani ya nuna cewa, a duk farkon shigowar sabuwar shekarar musulunci, Sheikh Muhajjdina kan fito da hasashe na yadda nazarinsu ya nuna yadda wasu muhimman al’amurra za su kasance a cikin shekarar. Ya kuma bayyana cewa, za a samu rikice-rikice tsakanin ƙasashen duniya za kuma a samu matsalar tattalin arziki da yawaitar sabani amma kuma akwai ƙashen da tattalin arzikinsu zai bunƙasa sosai a cikin shekarar.

Ya kuma bayyana cewa, za a samu sababbin masu arziki a wannan shekarar, ƙasashe masu ƙarfi za su yi ƙoƙarin danne wasu ƙasashen wanda kuma hakan zai gaza samuwa a kan haka za a samu rashe-rashen manyan mutane masu iko daga ƙasashen duniya, za kuma a samu bullar sabbin cututtuka a wasu ƙasashe “ba zamu iya bayyana sunayen suba saboda wasu dalilai”.

ADVERTISEMENT

Ya kuma ce, “Alhamdulillah musulunci zai ƙara samun karbuwa da ci gaba sosai a wannan shekara amma kuma al’ummar da suke cikin ƙunci da damuwa za su samu fita daga wannan ƙuncin daga ko wacce ƙasa suke a duniya”

“Buwaya da izza ta ƴan ƙasa za ta ɗan motsa a wannan shekarar haka masu neman kujeru ko shugabanci a ma’aikatu da guraran ayyukansu, da yawa yawansu za su samu cikar burukansu, harda masu neman promotion ma” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Yana da kyau kowa ya kula da dukiyarsa da ɗan abin daya mallaka ko domin da farko darajar kuɗin za ta iya ƙara yin ƙasa na 2 kuma duk abin da aka rabu dashi to dawo dashi a kusa zai yi wahala,” in ji shi..

Ya kuma bayyana cewa, za a samu yawaitar samun sabani tattare da ma’aurata da masoya zai ƙaru wanda hakan zai zama sanadin rabuwar aurarraki da dama don haka akwai buƙatar a ƙara kai zuciya nesa.

Duk yanayin tsilla tsilla da ake ciki akwai guraren da jama’a za su yi farin ciki bi’izinillahi ta’ala.

Sheikh Muhajjdina ya kuma bayyana cewa, za a samu yawaitar ciwon kai dana mara dana ciki a tsankanjin al’umma a wannan shekarar.

Ya kuma ce, karya alƙawaruka kan kuɗaɗe za su yawaita don haka a guji ɗaukar kuɗi masu yawa a bayar bashi, gwanda kwai in zaka iya taimaka wa mutum kawai ka taimaka shi da abin da zaka iya matsayin Kyauta.

Da ya koma a kan yadda zaben 2027 zai kasance, Sheikh Muhajjadina ya ce, za a yi zaben 2027 lafiya ba tare da tashin hankali ba, sai dai za a samu tashin hankali a yayin yaƙin neman zabe. ƴan siyasa da dama za su yi asara da dama kuma za su samu nasara kan a bin da suke nema na mulki. Aikan ya yi gargaɗi ga jami’an tsaro da ƴan siyasa da su jajirce wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata. Ya kuma ce za a samu tashin hankula a tsaskanin ƙungiyoyin ƴan ta’adda, saboda haka ya ce, jajircewar ‘jami’an tsaro zai taimaka wajen rage asarar rayukan da za a iya samu. Ya kuma yi gargaɗin cewa, za a samu ƙaruwar sace manyan jami’an gwamnati da manyan ƴan siyasa.

Za a samu wasu ƙasashen Afrika da za su faɗa lamarin juyin mulki da tashe tashen hankula, kamar yadda aka samu a shekarar da ta wuce

A bangaren tattalijn arziƙi, ya bayyana cewa, binciken su ya nuna cewa, za a samu ɗan matsin tattalin arziƙi a tsakanin al’umma amma daga baya arziƙi zai yalwata, farashin kaya zai sauko, talakawa za su fita daga matsin da suka shiga. Arziƙin wasu zai karye wasu kuma za su samu ɗaukaka a cikin shekƙarar.

Ya kuma shawarci shugabannin da suke rungumi aƙidar tausayawa talakawa domin matsawa talata a wannan shekarar zai iya kawo rikici da tashin hankalin da zai yi wuyar magani. Domin haka su san yadda za su tallafa wa talakawa a dukkan lokutta.

Daga ƙarshe ya buƙaci dukkan bangren al’umma su nemi masu ilimin taurari wajen neman fashin baƙi na yadda a al’murra suke tafiya domin kaucewa faɗawa halin da zai iya cutar da harkokin mulkinsu.

Tattalin arziki
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Tattalin arziki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Audu Sule Katagum Ya Rasu

Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Audu Sule Katagum Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.