ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

by Bello Hamza
2 months ago
World Bank on glass building. Mirrored sky and city modern facade. Global capital, business, finance, economy, banking and money concept 3D rendering animation.

World Bank on glass building. Mirrored sky and city modern facade. Global capital, business, finance, economy, banking and money concept 3D rendering animation.

Bankin Duniya, ta ɗora Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da na Tin Can Island, a mizanin ƙasashen 20, a duniya da suka ƙara haɓaka hada-hadar zirga-zirgar Kwantaina, a shekaru biyar, da suka gabata.

Wannan nasarar, za a iya danaganta da, ci gaba da namijin ƙoarin da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Ƙasa NPA, ke yi, na shirin zamanantar da Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar da ƙara ƙarfafa, ayyukansu.

Hakan ne ƙunshe, a cikin rahoton jaddawalin, ƙoƙarin da Tashoshin Jiragen Ruwan suka yi, wanda (CPPI) ya wallafa na na shekarar 2025.

ADVERTISEMENT

Bugu da ƙari, alƙaluman sun nuna cewa, wannan gagarumar nasarar da aka samu a Tashoshin Jiragen Ruwan biyu, musamman a ɓangaren ƙara inganta ayyuka da samar da sauƙin zirga-zirgar Jiragen Ruwan akan lokaci da kuma yadda ake kula da sauke kaya a Tashoshin, ya nuna a zahirance, na irin ingancin sauye-sauyen da Shugaban Hukumar ta NPA, Dakata Abubakar Ɗantsoho, ya ƙirƙiro da su aka samar a Tashoshin biyu, na jihar ta Legas.

Rahoton na haɗaka na CPPI da aka wallafa ya sanya Tashar Tin Can Island da ke a jihar Legas, kan mataki na 10 daga cikin sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya, da aka yi ƙoƙari, daga tsakanin 2020 and 2025.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

Haka zalika, Tashar Apapa, rahoton ya sanya ta kan mataki na 12, musamman duba da yan Kwantaina aka yi hada-hadar zirga-zirgar su a Tasahar, a cikin shekara ɗaya

Bugu da ƙari, Apapa a cewar rahoton ta yi matuƙar ƙoƙari inda makin ta ya kai kaso 35 ya kuma ƙaru zuwa  kaso 61 duk a cikin shekarar.

Rahoton na CPPI ya sanar da cewa, Tashar ta Tin Can Island ta samu maki 42 wanda kuma ya ƙaru zuwa maki 68 a shekarar 2020, inda kuma a shekarar 2025, ya kai maki 26.

Wannan gagarumar nasarar da aka samu, ta ƙara ɗora Nijeriya daga cikin sahun ƙasashen duniya, da ta mayar da hankalinta wajen ƙara haɓaka ayyukanta, da ƙara samar da kayan aiki a fannin, musamman kayan aiki, na zamani

Wannan sikelin da Bankin Duniya ya ɗora ƙasar nan, ya zo kan gaɓa na irin ƙoƙarin da ƙasar ke ci gaba da yi, na  ƙara bunƙasa hada-hadar kasuwancin ƙasar.

Hukumar ta NPA, ta kasance tana ci gaba da taimaka wa, wajen ƙara haɓaka, hada-hadar kasuwancin ƙasar, musamman duba da yadda aka samar da kayan aiki na zamani da ƙara inganta, ayyukan na NPA, ɓangaren fitar da kaya ƙetare da kuma fitar da su, ƙetare.

Ƙasar dai, ta samu gagaruwar nasara, a ɓangaren hada-hadar kasuwanci, tun a 2024, inda rahoton na baya-bayan nna, ya nuna cewa, ƙaruwar hada-hadar ta kai ta Naira tiriliyan 7.54, a zango na farko, na 2026.

Wasu masu ruwa da tsaki a fannin, sun bayyana cewa, ɗora ƙasar kan sikilen na baya-bayan nan, ya nuna cewa, an samu ne, saboda yawan zuba jari a kayan aikin Tashohin da kuma ƙara ɗaga daragarsu, ƙari da sauye-sauyen da aka samar, bisa nufin rage, duk wata koma baya da ake samu, a fannin.

Shugaban Hukumar ta NPA, Dakta Abubakar Ɗantsoho, ya ɗora samun wannan nasarar musamman kan zuba jari da samar da tsare-tsare, da Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da Ministan Bunƙasa Tattalin Arziki na Teku Dakta Adegboyega Oyetola, suka yi.

A cewarsa, Gwamnatin ta Shugaba Tinubu, na ci gaba da himmatuwa, wajen ƙara haɓaka fannin, tare da sanya kayan aiki na zamani,  a Tashin Jiragen Ruwan ƙasar, wanda hakan, ya ƙara taimaka ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci.

“Samar da kyakawan yanayin da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ga masu zuba jari a fannin, ya ƙara taimaka wa, a ɓangaren zuba jari, da kuma wanzar da sanya kayan aiki na zamani a fannin, tare da kuma ci gaba da goyon bayan da Ministan Bunƙasa Tattalin Arziki na Teku Dakta  Adegboyega Oyetola, wanda haka, ya kuma ƙara taimaka wa, wajen ƙara haɓaka tattalin arzikin Nijeriya,” Inji  Ɗantsoho.

Ya bayyana cewa, ɗora fannin kan sikelin zai kuma ƙara haɓaka fannin na ƙasar, a Afrika ta Tsakiya, tare da ƙara  bai wa masu zuba jari, ƙwarin Guiwa.

Apapa
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.