Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 11 a wasu hare-hare daban-daban da suka kai al’ummomin Taloka da Huda, da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
Wani mazaunin Taloka ya shaida wa Daily Trust cewa wasu da dama daga cikin ‘yan bindigar, ɗauke da muggan makamai akan babura kusan 20, sun mamaye al’ummar da misalin ƙarfe 12:30 na dare ranar Talata.
Ya ce mazauna garin sun farka ne bayan jin karar harbe-harbe, yayin da maharan suka shiga ƙauyen suna bi gida-gida domin sace mutane.
A cewar mazaunin, ‘yan bindigar sun fara shiga wani ɗaki da wasu matasa ke kwana. Duk da cewa matasan sun samu damar tserewa, amma maharan sun yi nasarar kama ɗaya daga cikinsu.
Daga nan, ‘yan bindigar sun shiga gidan wani Alhaji Yusuf, inda suka yi garkuwa da shi, ‘yarsa da kuma matar ɗansa. Haka kuma, sun kashe ɗaya daga cikin ‘yan uwansa, mai suna Abdullahi Dan Almajiri.
Maharan sun kuma kai hari gidan Mallam Gado Dan Tsohuwa, inda suka yi garkuwa da mata biyu da suka yi aure, kafin su wuce gidan Alu Kansila, inda suka yi awon gaba da ‘ya’yansa biyu, mace da namiji.
Mazaunin ya ce bayan sun tafi da mutane takwas, Alhaji Yusuf ya shaida wa ‘yan bindigar cewa saboda tsufansa ba zai iya ci gaba da tafiya da su ba. Daga nan ne maharan suka kashe shi tare da barin gawarsa a wurin, wadda daga baya mazauna yankin suka gano tare da yi masa jana’iza.
Mazauna yankin sun nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin gazawar jami’an tsaro da aka jibge a yankin wajen mayar da martani ga kiran neman agajin gaggawa a lokacin da ake kai hare-haren.














