ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Fitar Da Wani Shiri Na Shekaru 5 Domin Inganta Raya Kanana Da Matsakaitan Masana’antu

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 days ago
Sin

Kasar Sin ta fitar da wani shiri na karfafa ingancin kanana da matsakaitan masana’antu tsakanin shekarar 2026 zuwa 2030, wanda ke da nufin bunkasa harkokin kasuwanci da kirkire-kirkire da muhallin samun ci gaba.

Karkashin shirin wanda sassan gwamnati 10, ciki har da ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar suka fitar, ana sa ran zuwa shekarar 2030, kanana da matsakaitan masana’antu na kasar Sin za su samu ci gaba ta fuskar inganci da girma, inda jimilar kudin shigar manya daga cikinsu zai karu da kimanin kaso 15 cikin shekaru 5 masu zuwa.

Shirin ya bayyana kanana da matsakaitan masana’antu a matsayin muhimmin karfin da ke ingiza kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, yana kira da kokarin inganta tsare-tsaren samar da masana’antu masu inganci da hidimtawa jama’a da karfafa tsare-tsaren manufofi da dokoki da tabbatar da saukaka samun muhimman abubuwan dake inganta ayyukan masana’antu da karin goyon baya ga ci gabansu.

Bugu da kari, shirin na neman a ci gaba da inganta tsarin hidimomin kananan da matsakaitan masana’antu. Kana zuwa shekarar 2030, ana sa ran yawan yankunan hadin gwiwa tsakanin kanana da matsakaitan masana’antun kasar Sin da na ketare ya karu zuwa 50. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman

    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026

Next Post
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci