A ranar 7 ga watan Satumba mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje kasar Sin Mao Ning ta jagoranci taron manema labarai da aka saba gabatarwa inda ta bayyana cewa, daga 31 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumbar bana, babban darakta da shugaban majalisar kungiyar haramta amfani da sinadaran yaki masu guba, tare da wakilan din-din-din 12 na kungiyar da kuma manyan jakadu aka gayyata zuwa kasar Sin.
Yayin ziyarar an zagaya da su Hunchun, Dunhua, da kuma Halbaling da ke lardin Jilin domin ganewa idanunsu wuraren da ake lalata sinadaran yaki masu guba na Japan.Mao Ning ta kara da cewa, mamayar da Japan ta kai wa Sin a lokacin, ya haifar da mummunar annoba ga lafiyar al’umma tare da barin wani tabo da za a dinga tunawa da shi a tarihi.
A lokacin ziyarar dukkannin bangarorin sun fahimci irin mmumunar illar da sinadaran yaki da Japan ta yi amfani da su kan rayuka, da gidaje da kuma tsarin muhallin al’ummar kasar Sin.
Sun kuma goyi bayan kungiyar na haramta amfani da sinadaran yaki masu guba, kamar yadda yake a tsarin doka, tare da rokon kasar Japan ta cika alkawuran da ta dauka da gaggawa, sannan ta tabbatar da lalata dukkanin sinadaran da ta bari a Sin A daya banagaren kuma, Mao Ning ta bayyana yadda kafofin watsa labarai na duniya suka nuna damuwa kan ibita’in da aka samu a Gyirong, tare da fatan cewa za su je wurin domin tattaunawa da al’umma da kuma dauko rahoto.
Kazalika kasar Sin ta gayyaci wakilan manyan kafafan yada labarai 8 na duniya zuwa wuraren da ibtial’in ya fi shafa, domin ganewa idanunsu irin ci gaban da ake samu a kokarin cetowa da sake ginawa da kuma farfado da wuraren da ibtila’in ya shafa.
Ta kuma kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari domin lalubowa da kuma ceto wandanda abin ya rutsa da su, tare da bayar da cikakken rahoto kan yadda aikin ke gudana. (Suleiman Ibrahim)














