Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta bayyana a yau Lahadi cewa, kasar ta taka muhimmiyar rawa a taron ministocin kula da cinikayya na kasashen G20, wanda aka yi a Milwaukee na Amurka a ranekun 30 ga Satumba da 1 ga watan Oktoba.
Wani kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka, inda ya ce yayin taron baki daya, Sin ta rungumi dabarar hadin gwiwa da yin komai a fili, kuma ta shiga an dama da ita cikin tattaunawar da aka yi kan batutuwa daban-daban, tare da tuntubar juna da sauran mambobi, da kuma taka cikakkiyar rawa wajen inganta tattaunawa da hadin gwiwa.
A cewar kakakin, Sin ta kiyaye ka’idoji da kare muradunta da na kasashe masu tasowa da kuma aiki domin inganta hadin kai da hadin gwiwar kasashen G20. (Fa’iza Mustapha)













