Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane biyar da ake zargi da ɓatawa tare da yaga fastocin yaƙin neman zaɓe na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wasu sassan birnin Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kama waɗanda ake zargin ne a yayin da suke tsaka da ɓarnata fastocin a kan manyan titunan birnin, biyo bayan sintiri da kuma bayanan sirri da jami’an suka samu kan ayyukan ɓata-gari da ke ƙoƙarin tayar da tarzoma ta siyasa.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar ya tabbatar da kamen, inda ya bayyana cewa rundunar ba za ta zuba ido tana kallon duk wani aiki da zai iya haifar da rashin jituwa ko tashin hankali a tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa ba, musamman a daidai lokacin da yanayin siyasa ke ƙara ɗaukar ɗumi.
Rundunar ta bayyana cewa mutanen biyar na tsare a sashin binciken manyan laifuka inda ake ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi a kansu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike domin fuskantar hukuncin da ya dace da laifin da suka aikata.
Rundunar ƴansandan ta yi kira ga matasa da magoya bayan jam’iyyun siyasa a jihar da su guji shiga harkokin siyasar ɓarna ko ɗaukar doka a hannunsu, tana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu da laifin kawo cikas ga zaman lafiyar jihar zai fuskanci fushin doka ba tare da nuna bambanci ba.













