Maaikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, yayin da ake wata gaba na sabon mafari a tarihi, kasar Sin za ta hada hannu da kasashen Afrika, mambobin dandanlin tattauna hadin kan Sin da Afrika (FOCAC), wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taron dandalin, domin alummomin bangarorin biyu su kara amfana.
A makon da ya gabata ne aka yi nasarar gudanar da taron dandalin na FOCAC.
- ’Yan Kasuwa Daga Kasashe Da Yankuna 119 Sun Halarci CIFIT Karo Na 24
- Jami’in Kenya: Taron Dandalin FOCAC Zai Zurfafa Dangantakar Sin Da Kenya
Kakakin maaikatar Mao Ning ce ta bayyana haka, tana cewa, a yan kwanakin da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar yayin taron FOCAC cewa, kasarsa za ta aiwatar da matakin taimakawa nahiyar Afrika kawar da barazanar nakiyoyi.
A cewar Mao Ning, a shirye kasar Sin take ta karfafa hadin gwiwa kan harkokin kawar da nakiyoyi da kasashen Afrika, ta hanyar taimakon kayayyaki da bayar da horo da bayar da jagoranci yayin da ake gudanar da aikin da sauran hanyoyi, domin taimakawa nahiyar kawar da hadarin dake tattare da nakiyoyi nan bada jimawa ba, ta yadda zaa tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da samun ci gaba mai dorewa. (Faiza Mustapha)