ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Zai Yiwu A Cimma Yarjejeniya Ba Tare Da Sanya Batun Lebanon Ba —Iran

by Rabi'u Ali Indabawa
3 weeks ago
Iran

Iran ta ce ba zai yiwu a cimma duk wata yarjejeniyar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ba tare da an sanya batun tsagaita wuta a Lebanon ba, lamarin da ke haddasa sarkakiya a kokarin da Amurka ke yi na kawo karshen rikicin yankin a diflomasiyyance.

Jagoran wakilan Iran a tattaunawar lalubo zaman lafiya da ake yi, Mohammad Bagher Kalibaf ya ce Iran ba za ta rattaba hannu akan duk wani tsarin diflomasiyya da Amurka ba idan har bai bada tabbbacin tsaro ga kawayenta na yankin ba.

Iran ta jaddada cewa dakakar da rikicin Lebanon shi ne babban sharadin da ba za ta lamunci sabawa ba akan duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da a za a cimma a Gabas ta Tsakiya.

ADVERTISEMENT

Wannan  tsatsaurar matsaya ta Iran ce ta sanya Amurka bijirowa da wani sabon kudiri na neman kawo karshen yaki tsakanin Isra’ila da Hezbollah a Lebanon.

Kudirin na Amurka ya zayyana yadda za a kawo karshen rikicin a hankali, tsarin da za a fara da bukatar Hezbollah ta dakatar da hare-haren da take kai wa Isra’ila , kana Isra’ilar ta sassauta matakan sojin da take dauka a babban birnin Lebanon.

LABARAI MASU NASABA

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

Sai dai kudirin na Amurka na fuskantar turjiya ta fannoni daban-daban, inda a cikin Lebanon an samu rarrabuwar kawuna a jagorancin siyasar kasar, saboda a yayin da shugaba Joseph Aoun yake yunkurin gabatar da kudirin, kakakin majalisar dokokin kasar, Nabih Berri ya yi watsi da shi, yana mai cewa sai Isra’ila ta fara dakatar da hare-hare.Kasashen Da Darajar Kudadensu Suka Fadi Da Wadanda Nasu Suka Tashi Sanadiyyar Yakin Iran

Lokacin da rikicin da ya hada Amurka da Isra’ila da Iran ya barke a karshen watan Fabrairu, tasirinsa bai tsaya a Gabas ta Tsakiya kadai ba.

A yayin da rikicin ya kawo cikas ga jigilar kaya ta teku da kuma zirga-zirgar kasuwanci a duniya, farashin mai ya tashi sosai.

Wannan kuma ya janyo hauhawar farashin kaya a kasuwannin duniya, abin da ya girgiza tattalin arzikin kasashe da dama.

A irin wannan yanayi na rashin tabbas, wasu masu zuba jari sun guji sanya kudi a kasuwanni masu hadari, musamman a kasashe masu tasowa.

Maimakon haka, sun koma saka kudinsu a Dalar Amurka, wadda ake dauka a matsayin amintaccen mafakar kudi a lokutan rikici.

Wannan faduwa da tashin darajar kudi ya yi tasiri kai tsaye ga darajar kudaden kasashe da dama.

Wasu kudaden kasashe sun yi rauni sosai, wasu kuma sun kasance cikin sauyin da ba tabbas, yayin da wasu kadan suka samu karin karfi.

Masanin tattalin arziki dan Brazil André Perfeito, wanda ke jagorantar kamfanin ba da shawara APCE, ya ce hauhawar farashin mai “yana shafar kowa, amma faduwa da tashin darajar kudi na iya kara tsananta ko kuma rage wannan tasiri.”

Wadanda abin ya fi shafa sosai

Kasashen da ke shigo da makamashi da yawa, musamman mai, suna daga cikin wadanda kudadensu suka fi fuskantar matsin lamba.

Cikin wadannan kasashe akwai Indiya, Indonesia, Philippines, Thailand da Masar.

Dukkansu sun fara fuskantar karin matsin tattalin arziki sakamakon tashin farashin mai da kuma karancin samun kudin waje.

Yayin da masu zuba jari ke mayar da kudadensu zuwa Dalar Amurka, bukatar wasu kudaden kasashe ta ragu.

Wannan ya sa darajarsu ta fadi. Idan darajar kudi yana faduwa da tashi, biyan bashi da aka karba da Dalar Amurka ma yana kara tsada.

Haka kuma, mai da sauran kayayyaki da ake shigo da su daga waje wadanda sau da yawa ana farashinsu da Dalar Amurka ne musamman saboda tasirin rikice-rikice da ke hana zirga-zirga a mashigar Hormuz suna kara tsada idan darajar kudin kasa ta ragu.

Wannan na nufin abubuwan da ake shigo da su kamar makamashi, robobi da takin zamani suna yin tsada.

Daga nan kuma, farashin abinci da kayayyakin yau da kullum a kasuwanni yana karuwa.

A Indiya, Rupee ya ragu da kusan kashi 5 cikin 100 a kan Dalar Amurka tun bayan fara rikicin, inda ya kai matakin da bai taba kaiwa ba a lokuta da dama yayin da farashin mai ke tashi.

Ko da kafin rikicin, kudin Indiya ya riga ya fara yin rauni, amma wannan ya kara tsananta yanayin.

Wasu bankunan kasashe sun mayar da martani ta hanyar kara yawan riba da kuma sayar da Dalar Amurka da aka ajiye domin tallafa wa kudin kasarsu.

Bankin Indonesia ya yi amfani da duka matakan da suka hada da sayar da daloli a kai-a kai tare da sayen Rupiah domin kara bukata da daga darajarsa.

Idan aka kara yawan ribar banki, mutane suna samun riba mai yawa a ajiyarsu. Amma a gefe guda, hakan yana nufin biyan basussuka kamar lamunin gida da sauran rance zai kara tsada.

Hawa da saukar darajar kudade

Wasu kudaden kasashe kuwa sun fi fama da karyewar darajar kudi sosai, suna hawa da sauka cikin sauri.

Kasashen da abin ya fi shafa sun hada da Afrika ta Kudu da Colombia da Chile da Medico.

Yawanci irin wadannan kudade suna faduwa da tashi idan masu zuba jari suka koma amfani da Dalar Amurka, amma suna iya farfadowa idan farashin kayayyakin masarufi kamar mai ya tashi ko kuma masu zuba jari suka sake nuna sha’awa.

Kasashe masu fitar da makamashi irin su Brazil da Malaysia sun samu dan anfani daga tashin farashin mai, wanda ya kara kudaden shiga da sha’awar masu zuba jari.

Bankuna kamar Goldman Sachs da Bank of America sun bayyana cewa ana yawan sayen takardun bashin gwamnati da hannayen jari na Brazil.

Sai dai masana sun ce hauhawar farashin mai na iya kara tashin farashi a Brazil, wanda zai iya hana rage kudin ruwa da kuma shafar shigowar jari.

Haka kuma Brazil na shigo da man fetur da dizal daga waje, abin da ke kara tsadar mai a cikin kasar.

Masana sun ce rashin tabbas game da zaben shugaban kasa na watan Oktoba a Brazil na iya kara raunana kudin kasar saboda masu zuba jari na nuna tsoro.

Iran
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

MASU ALAKA

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya
Kasashen Ketare

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

June 23, 2026
Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya
Kasashen Ketare

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

June 22, 2026
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran
Kasashen Ketare

Iran Ta Ce Shirinta Na Makamai Masu Linzami Ba Ya Cikin Tattaunawa Da Amurka

June 18, 2026
Next Post
ADC Na Zawarcin Gawuna Domin Ya Yi Wa Jam’iyyar Takarar Gwamnan Kano A 2027

ADC Na Zawarcin Gawuna Domin Ya Yi Wa Jam’iyyar Takarar Gwamnan Kano A 2027

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Mataimakin Babban Sakataren MDD Ya Yaba Wa Dabarun Sin Kan Mulkin Kasa

Tsohon Mataimakin Babban Sakataren MDD Ya Yaba Wa Dabarun Sin Kan Mulkin Kasa

June 26, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Sabbin Matakan Dakile Haɗura A  Titin Bypass

Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Sabbin Matakan Dakile Haɗura A Titin Bypass

June 26, 2026
Disu

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Sin Ta Habaka Karfin Soja Ne Don Kare Ikon Mallakar Kasa Da Muradun Ci Gaba

Sin Ta Habaka Karfin Soja Ne Don Kare Ikon Mallakar Kasa Da Muradun Ci Gaba

June 26, 2026
Iran

Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Fara Aikin Gina Mayankar Zamani A Garin Jos

June 26, 2026
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Amfani Da Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Ta Fakewa Da Zargin “Kwadagon Tilas”

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Amfani Da Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Ta Fakewa Da Zargin “Kwadagon Tilas”

June 26, 2026
NDC Ta Ce Za Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Rajistarta

NDC Ta Ce Za Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Rajistarta

June 26, 2026
An Fitar da Jadawalin Wasannin Zagayen Farko Na Gasar Carabao Cup ta 2026/2027

An Fitar da Jadawalin Wasannin Zagayen Farko Na Gasar Carabao Cup ta 2026/2027

June 26, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ba Ta Da Hujjar Umartar INEC Ta Soke Rajistar Jam’iyyu —Uban Doman Lafiya

June 26, 2026
Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

June 26, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.