Za a bude gasar wasannin motsa jiki karo na biyu na mutum-mutumin inji masu siffar dan adam na kasa da kasa a ranar 22 ga watan Agusta a filin wasannin kankara na kasa mai suna “Ice Ribbon” dake birnin Beijing, hedkwatar mulkin kasar Sin. Gwamnatin birnin Beijing da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da sauransu ne suka shirya gasar .
Wannan gasa ta jawo kungiyoyi 666 da mutum-mutumin inji masu siffar dan adam 2056 daga kasashe 16 na nahiyoyi 6, inda adadin kungiyoyi ya karu da kashi 138 bisa dari idan aka kwatanta da na farko, kuma adadin mutum-mutumin inji ya ninka sau 4. Mutum-mutumin inji na kungiyoyin Amurka, Jamus, Japan da mutum-mutumin inji 1975 daga kungiyoyi 641 daga kamfanonin Sin 157 za su fafata tare.
Gasar karo na biyu ta fadada nau’ikan gasanni da yawan kungiyoyi masu shiga idan aka kwatanta da ta farko. Kuma bisa ajandar gasar, za a gudanar da wasanni 1301 bisa nau’ikan gasanni 51. (Amina Xu)














