Da safiyar yau Jumma’a, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai mai jigon “Fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15”, inda jami’in m’aikatar kudi ta Sin ya gabatar da wasu batutuwan dake da alaka da aiwatar da manufar harkokin kudi mai inganci, da habaka ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai inganci.
A gun taron, Liao Min, mataimakin ministan kudi na Sin, ya bayyana cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, an ci gaba da inganta karfin manyan manufofin harkokin kudi kan daidaita tattalin arziki, wanda hakan ke tallafawa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai inganci da kuma cimma dorewar harkokin kudade, wanda kuma ya kara jaddada muhimmancin harkokin kudade a matsayin tushe da ginshikin shugabancin kasa.
Yayin da ake aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, Sin za ta yi kokarin gina tsarin harkokin kudi mai karfi, kwanciyar hankali, daidaito, kuma mai dorewa, ta yadda zai ba da tabbaci a fannin harkokin kudi don samun ci gaba mai muhimmanci yayin cimma zamanantarwa bisa tsarin gurguzu.
Bugu da kari, a wannan shekarar, Sin ta kaddamar da matakai a jere don sanya harkoki da hada-hadar kudi kara yawan bukatar da ake da ita a cikin gida. Game da haka, Liao Min ya bayyana cewa, bayan aiwatar da matakan, a cikin watanni shida da suka gabata, kimanin mutane miliyan 113, ciki har da kamfanoni miliyan 6.22, sun amfana da manufofin. (Safiyah Ma)














