ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga Sayar Da Kayayyakin Da Ba a Sarrafa Ba Zuwa Kera Kayayyaki Masu Karin Daraja: Yadda Sin Ke Taimakawa Najeriya Canza Yanayin Cinikinta

by Sulaiman and CGTN Hausa
3 weeks ago
Sin

Sin ta fara aiwatar da manufar soke harajin fito gaba daya ga kasashe 53 na Afirka da suka kulla dangantakar diplomasiyya da ita daga ran 1 ga watan Mayun bana. Bayan watanni uku da rabi, Najeriya ta amfana sosai da wannan manufa. A kwanan nan kafafen yada labarai na kasar na cewa, a rabin farkon bana, yawan kayayyaki da Najeriya ta fitar da su zuwa kwasuwannin kasar Sin ya karu da kashi 80%, inda darajarsu ta kai dala biliyan 2.3, kuma an samu karuwar da ta wuce kashi 40% a watannin Mayu da Yuni. Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi amfani da wannan dama don inganta kwaskwarima ta hanyar karkata tsarinta na fitar da kayayyaki, wato daga fitar da danyen kayayyaki ko kayayyakin da aka dan sarrafa zuwa fitar da kayayyakin noma da kayayyakin ma’adanai masu karin daraja, da kayayyakin masana’antu da aka sarrafa su sosai.Batun nan ya bayyana yadda aka hada tsarin bude kofa bisa manufofin ketare da Sin ke dauka da bukatun neman ci gaba na kasashen Afirka tare.

Ministan ma’aikatar noma da samar da isasshen abinci na Najeriya Aliyu Sabi Abdullahi, a wani taron karawa juna sani kan “Manufar soke haraji ta Sin da sauyin tsarin tattalin arzikin Afirka”, wanda aka gudanar kwanan nan a Najeriya, ya ce “Manufar soke haraji kadai ba za ta tabbatar da samun ci gaban da muke bukata ba”. Kalaman ministan sun bayyana abin da Najeriya ke karin bukata bisa matakin da Sin ke dauka, watau baya ga manufar soke haraji, Sin na samar da damarmakin da ke taimaka wa Najeriya wajen inganta karfinta na cin moriya tare.

Yayin taron, jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya bayyana cewa, bangaren Sin yana son ba da tallafin fasaha a fannin samar da kayayyaki, don kara ingancin kayayyakin Najeriya da samun damar fadada shiga kasuwar Sin. Wannan shi ne mabudin fadada hadin gwiwar Sin da Afirka daga “mu’ammalar ciniki” zuwa “bunkasa karfi tare da cin moriya tare”.

ADVERTISEMENT

Alal hakika, fa’idojin hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Najeriya sun riga sun bayyana sakamako na a zo a gani. Jakada Yu ya ce, masu fitar da kayayyaki na Najeriya za su iya yin tsimin kudin haraji kusan dala dubu 11 a kowane ton 100 na ridin da za su fitarwa Sin, kana za a yi tsimin kudin haraji kusan dala dubu 450 idan aka fitarwa Sin gutsurarrun kashin saniya tan dubu 7 a kowace shekara. Ban da wannan kuma, a ranar farko da aka fara aiwatar da manufar, ’yan kasuwar Najeirya sun yi tsimin kusan dala dubu 300 wajen fitar wa Sin iskar Propane mai ruwa tan dubu 23.

Wadannan alkaluma suna nufin cewa, kudin shigar manoman Najeriya ya karu, kwarin gwiwar masana’antar sarrafa kayayyaki ya karu, kuma guraben ayyukan yi sun karu.Canji mafi zurfi ya zo a bangaren yi wa tsarin cinikayya kwaskwarima a Najeriya. Da ma Najeriya tana fitar da kayayyakin noma da ba a sarrafa su ba da danyen ma’adanai zuwa Sin, amma bayan Sin ta aiwatar da wannan manufa, ta bai wa Najeriya damammakin fitar da kayayyakin noma na musamman da kayan ma’adanai masu karin daraja da aka sarrafa, zuwa kasuwar Sin cikin sauri.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Hadin gwiwar Sin da Najeriya ba wai kawai “hadin kai ne a kan ababen more rayuwa” ba, har ma da “zurfafa hadin gwiwa a bangaren masana’antu da kasuwa”, bayan rabin karni da kafuwar dangantakarsu ta diplomasiyya. Kuma Sin ba samar wa Najeriya damar shiga kasuwa kadai ta yi ba, har ma da taimaka mata wajen kafa cikakken tsari kan kowane nau’in kaya da za ta fitar zuwa Sin, bisa tallafin kimiyya da fasaha da hadin gwiwar masana’antu, ta yadda Najeriya za ta daina fitar da danyen ma’adinai da kayayyakin da ba a sarrafa ba, matakin da ya bayyana sabon nau’in hadin gwiwar Sin da Afirka wanda ya zama abin koyi, wato hadin gwiwa da cin moriya tare.(Marubuciya:MINA)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Jimillar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice Ta Sin Da Sauran Membobin APEC Ta Wuce Yuan Tiriliyan 18 A Watanni Bakwai Na Farkon Bana

Jimillar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice Ta Sin Da Sauran Membobin APEC Ta Wuce Yuan Tiriliyan 18 A Watanni Bakwai Na Farkon Bana

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.