ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kawar Da Haraji Kan Hajojin Afirka Da Ake Shigarwa Kasar Sin Zai Samar Da Sabbin Damammakin Ci Gaba Ga Kasashen Nahiyar

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Haraji

Wata sanarwa da ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar, ta ce sabon matakin da gwamnatin Sin ta sanar na kawar da daukacin harajin fito kan hajojin dake shiga babbar kasuwar kasar daga kasashen Afirka, zai taimakawa kasashen nahiyar da sabbin damammakin samun ci gaba, tare da tallafa musu da zarafin kaucewa yanayin tangal-tangal da tattalin arzikin duniya ke fuskanta yanzu haka.

Sanarwar wadda ma’aikatar ta fitar a jiya Laraba, ta kuma ce wannan mataki zai samar da damammaki a fannoni daban daban, ciki har da rage tsadar hajojin Afirka dake shiga kasuwannin Sin, wanda hakan zai ba su damar inganta gogayyar kasuwa.

Kazalika, sanarwar ta ce matakin janye harajin zai sanya karin ’yan kasuwa Sinawa, da sauran abokan huldar cinikayya su kara zuba jari a Afirka, da shigar da kudade, da fasahohi, da kayayyakin aiki da kwarewar gudanarwa, wanda hakan zai kara kyautata hajojin da ake sarrafawa a nahiyar gabanin fitar da su zuwa kasar Sin.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari, ma’aikatar cinikayyar ta Sin ta ce janye harajin wata dabara ce da za a aiwatar daki-daki, a gabar da Sin da kasashen Afirka masu ruwa da tsaki ke aiki tukuru, wajen ganin sun kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar hadin kai ta raya tattalin arziki tsakanin Sin da Afirka domin samar da ci gaban bai daya.

Har ila yau, yarjejeniyar za ta taimaka wajen kafa tsarin raya cinikayya da zuba jari na dogon lokaci, bisa daidaito, da tabbaci tsakanin Sin da kasashen Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Bugu da kari, tasirin ta bai tsaya ga warware damuwar kasashen Afirka game da harajin fito kadai ba, har ma zai biya bukatun kasashen nahiyar a fannonin kawar da shingayen da ba na harajin fito ba, da kyautata damar gudanar da cinikayya tare da janyo jarin waje. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)

Haraji
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Haraji
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

MASU ALAKA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Next Post
APC Ta Ƙara Wa’adin Sayar Da Fom Ɗin Takara Zuwa Litinin Da Talata

Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.