ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Wata ɗaliba mai shekaru 19, Rebecca Kambai, wadda ke karatun mataki na biyar a Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya da ke Azare (FUHSA), ta rasa ranta sakamakon wani hatsarin mota da direban ya tsere daga wurin a kan hanyar Bauchi–Jos a Jihar Bauchi.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata yayin da Rebecca ke dawowa gida bayan karɓo kayanta da aka kawo mata daga makaranta.

Majiyoyin iyalinta sun bayyana cewa Rebecca ta dawo gida hutun makaranta ne, amma daga baya ta gano ta manta wasu kayanta a harabar jami’ar. Abokanta suka shirya aka kawo mata kayan zuwa tashar mota da ke kusa da Awala Hotel a Bauchi, inda ɗan’uwanta ya kai ta a babur domin karɓarsu.

ADVERTISEMENT

Bayan sun karɓi kayan suna kan hanyarsu ta komawa gida ne Rebecca ta karɓi tuƙin babur ɗin, amma da suka isa gaban Police Officers’ Mess a yankin New GRA, wata motar Sharon ta buge su sannan ta tsere.

An ce Rebecca ta buga kanta da ƙasa, lamarin da ya haifar mata da mummunan rauni a ƙoƙon kai wanda ya yi sanadin rasuwarta nan take, yayin da ɗan’uwanta ya samu raunuka.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Rahoton Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ya tabbatar da cewa hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 5:15 na yamma ranar 14 ga Yuli, 2026, kuma jami’an ceto sun isa wurin cikin mintuna goma bayan samun rahoton.

An garzaya da wanda ya jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) domin kula da lafiyarsa, yayin da aka ajiye gawar Rebecca a ɗakin ajiyar gawa na asibitin.

Mahaifiyar marigayiyar, Doris Kambai, ta bayyana rasuwar ‘yarta a matsayin babban rashi ga iyalinta. Ta ce Rebecca ita ce ƙaramar ‘yarta kuma tana da matuƙar basira da hazaƙa. Ta gode wa duk waɗanda suka jajanta wa iyalinsu tare da yi musu addu’a a wannan lokaci na alhini.

A halin yanzu, direban motar Sharon da ake zargi da haddasa hatsarin ya tsere, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin gano shi tare da cafke shi domin fuskantar hukunci.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba - Tsohon Shugaban NAHCON

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.