A ’yan kwanakin baya bayan nan, wani rahoto daga rukunin masanan Amurka, ya yi ikirarin cewa matakin takaita baiwa dalibai Sinawa bizar karatu a Amurka, zai yi matukar tallafawa dalibai Amurkawa, tare da inganta tsaron kasar.
Wannan rahoto ya yi nuni da aniyar masanan kasar ta siyasantarwa, da kuma mayar da batun musayar ilimi wani makamin danniya, ta fakewa da batun tsaron kasa. Wani abun lura a nan shi ne yayin da rahoton ke ganin rage adadin daliban kasa da kasa dake zuwa Amurka karatu a matsayin wata babbar nasara, bangaren Amurka ya kawar da kai daga illar da matakin zai haifar.
Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta rage adadin biza nau’in F‑1 da kasar ke baiwa dalibai ’yan asalin kasashen Indiya, da Sin tsakanin watan Mayu zuwa Agustan shekarar 2025, idan an kwatanta da adadin da ake bayarwa a shekarun baya.
Abun tambaya dai shi ne ta yaya daliban kasa da kasa za su iya illata tsaron Amurka? Wancan rahoto bai gabatar da amsar wannan tambaya ba. To sai dai kuma, wasu sassa na Amurkawa na ganin bude kofar musayar dalibai na iya wanzar da kyakkyawar gogayya a fannin nazari da ayyukan bincike.
Yayin da wasu sassan kuma ke ganin daliban kasa da kasa masu karatu a Amurka na mamaye guraben ayyukan yi da kasar ke da su. Wasu na ganin daliban kasa da kasa na bayar da gudunmawar ingiza ci gaban kirkire-kirkire, yayin da wasu ke ganinsu a matsayin barazana ga tsaron kasa.
Hakan a cewar wasu masu fashin baki, shaida ce dake nuna tarin sabanin ra’ayi dake akwai tsakanin al’ummun Amurka.
A daya hannu kuma, sanannen abu ne cewa daliban kasa da kasa na shigar da tarin kudaden karatu cikin tattalin arzikin Amurka, kuma babu wata shaida da za ta iya tabbatar da zarginsu da aikata leken asiri ko kasancewa barazana ga tsaron kasar.
Daliban kasa da kasa na ingiza ayyukan bincike, da nazari, da koyarwa a fannoni mabanbanta, har ma su kansu Amurkawa sun amince cewa rashin irin wadannan dalibai na iya gurgunta tsarin karatu da raya ilimi na Amurka. Yayin da Sin da Amurka ke aiwatar da musayar dalibai, dukkannin sassan biyu na cin gajiyar fadada kwarewa a fannonin ilimi daban daban.
Amma bayyana wannan tsari a matsayin barazana ga tsaro babban kuskure ne da zai illata moriyar ita kanta Amurka, kuma zai iya zama wani mataki na farfado da yakin cacar baka, da tauye damar al’ummun kasa da kasa ta yin gogayya bisa tsarin da aka jima da amincewa da shi. (Saminu Alhassan)














