Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta soki kokarin Japan na gangancin fadada karfin soji, tana mai bayyana hakan a matsayin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.
Kakakin ma’aikatar Chen Xi ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a, lokacin da yake amsa tambaya game da batun gwaje-gwajen makamai masu linzami da Japan ta yi a baya-bayan nan da ikirarin ministan tsaron Japan cewa, makamai masu linzami masu cin dogon zango na zama wani bangare na karfin Japan na tunkarar hare-hare.
Yayin wani taron manema labarai na daban na ma’aikatar harkokin wajen Sin a yau, kakakin ma’aikatar Lin Jian ya ce a bayyane jami’an Japan ke neman karya ka’idoji uku na rashin mallakar nukiliya suna caca da makomar rayuwar Japanawa miliyan 100.
Ya ce ya kamata hukumomi masu mulkin Japan su saurari kiran jama’a, su daina ganganci game da batun nukiliya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














