ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kamo Ɗan Takarar Gwamnan Bauchi Na NDC, Ibrahim Kashim

by Sadiq
3 months ago

Kotun Majistare da ke zamanta a Jihar Bauchi, ta bayar da umarnin kama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar, Barrista Ibrahim Kashim Muhammad, wanda kuma tsohon Sakataren Gwamnatin jihar ne.

Alƙalin kotun, Abdulmumini Adamu ne, ya bayar da umarnin a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2026, a wata shari’a da lauyoyi biyu, Barista Ahmed Sani da Barista Hussaini Saraki, suka shigar a kansa.

Suna zargin sa da ɓata musu suna da mutunci.

ADVERTISEMENT

Kotun ta ce an ba da umarnin kama shi ne domin a tilasta masa ya bayyana a gaban kotu, bayan roƙon lauyan masu ƙara.

Bayan haka, kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2026, inda ake sa ran zai halarci zaman kotun na gaba.

LABARAI MASU NASABA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Lauyoyin da suka shigar da ƙarar sun ce batun ya samo asali ne daga wasu kalamai da ake zargin Kashim ya yi a wata hira ta gidan talabijin na Zamani TV a ranar 3 ga watan Yuni, 2026.

Sun ce a cikin hirar, ya yi wasu maganganu da suka shafi lauyoyin, inda suka ce kalaman ba gaskiya ba ne kuma sun ɓata musu suna a idon jama’a.

Masu ƙarar sun ce kalaman sun sa jama’a suka fara shakkar gaskiyarsu da aikinsu.

Sun kuma shigar da ƙara kan laifin ɓata suna da yada ƙarya bisa dokar Jihar Bauchi.

A nasa martanin, Barista Ibrahim Kashim ya ce bai guje wa kotun ba.

Ya bayyana cewa ya riga ya shirya tafiya zuwa Abuja kafin gabanin kai masa sammacin kotu.

Ya ce ya ba lauyansa umarni ya wakilce shi, sannan ya nemi a ba shi sabon lokaci domin ya halarta da kansa.

Ya ƙara da cewa yana mutunta kotu kuma zai halarci shari’ar a lokacin da aka tsara, yana mai cewa zai kare kansa bisa doka.

MASU ALAKA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai
Labarai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku
Labarai

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro
Labarai

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Next Post
Kano: Hisbah Ta Tantance Mutane 720 Waɗanda Za A Yi Wa Auren Gata

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.