A cewar kididdigar hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin, kudaden shiga na fina-finai a lokacin hutun murnar ranar cika shekaru 77 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin na shekarar 2026 sun kai yuan biliyan 1.165, inda kowace rana cikin kwanaki 7 a jere, kudaden shiga suka wuce yuan miliyan 100, kuma adadin masu kallo ya kai miliyan 31.99, kason kudaden shiga na fina-finan cikin gida ya kai kashi 78.7%.
Ya zuwa ranar 7 ga watan, jimillar kudaden shiga na fina-finai na duk shekara sun kai yuan biliyan 30.746, kuma adadin masu kallo ya kai miliyan 784. (Amina Xu)
ADVERTISEMENT














