ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kungiyar Malaman Jami’ar AFUSTA Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

by Sulaiman and Umar Faruk Birnin Kebbi
2 months ago
AFUSTA

Kungiyar Malaman Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero, a Jihar Kebbi za ta tsun duma fage yajin aikin gama-gari na dindindin idan har gwamnatin jihar Kebbi ta kasa biyan hakkokin mambobinta.

An bayyana matsayin kungiyar ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar 22 ga Afrilu, 2026, a sakatariyar ASUU-AFUSTA da ke Aliero.

Sanarwar da aka fitar a wajen taron na dauke da sa hannun shugaban reshen Kungiyar na Jami’ar Dakta Musa Isah Fakai da sakataren Kungiyar Dakta Gado Abubakar A. A jawabin da ta yi wa manema labarai a wajen taron, ASUU-AFUSTA ta ce ya zama wajibi a sanar da jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi kan matsalolin da suka dabai baye Jami’ar suka kuma kawo cikas ga harkokin ilimi a Jami’ar sama da shekaru goma.

ADVERTISEMENT

“Haka kuma, ya zama jawabi ga jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a Jihar Kebbi domin yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakan da suka dace don magance matsalar ’yan kwadago da ta addabi Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio, da ke a karamar hukumar Aliero,” in ji kungiyar.

Kungiyar ASUU-AFUSTA ta ruwaito Gwamna Nasir Idris, wanda ta kira shi da “Comrade Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu),” inda ta ambato shi yana cewa, “mafi yawan nasarorin da ake samu ana samun su ne ta hanyar gudanar da aikin kwazo da kuma jajirce wa.

LABARAI MASU NASABA

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Kazalika Kungiyar ta tuno da tarihin sunan jami’ar, inda ta bayyana Abdullahi Fodio a matsayin “malami kuma shugaban da ya share hawayen marasa galihu da marayu tare da baiwa marasa karfi karfi”.

Kungiyar ta ce “Ya yi kokari sosai wajen ilmantar da jama’ar sa, bai taba yarda da wasu da ke karkashinsa su yi wasa da shi ko kuma a tsaya tsakaninsa da ‘yancin talakawansa ba,” in ji kungiyar.

ASUU-AFUSTA ta Kara da cewa ta Kara gabatar da korafi korafen ta tun a ranar 15 ga Afrilu, 2026, ga Hukumar Gudanarwar Jami’ar, Majalisar Mulki ta Jami’ar, da kuma Ma’aikatar Ilimi mai zurfi ta Jihar Kebbi amma har yanzu kamar an shuka dusa.

Kungiyar ta ce “A Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio, da ke garin Aliero, akwai matsaloli da dama da ke lalata yanayi mai kyau na koyarwa sun kasance ba a warware su ba har tsawon shekaru goma,” in ji kungiyar.

Bugu da Kari Kungiyar ta zayyana wasu matsalolin da suka kai har guda tara, wanda ya fara da rashin aiwatar da sabon tsarin biyan albashin ma’aikatan ilimi na jami’o’in Nijeriya. An yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ASUU wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Junairu, 2026, inda ta warware duk wasu matsaloli da suka kunno kai daga yarjejeniyar FGN da ASUU na shekarar 2009.

“Duk da cewa kungiyar ta mika yarjejeniyar ga hukumar Gudanarwar ta Jami’ar AFUSTA, ga Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar, da kuma Ma’aikatar Ilimi mai zurfi ta Jihar a ranar 15 ga Janairu, 2026, tun bayan gabatar da yarjejeniyar ga wadanan hukumomin ba a samu wani sakamako ba, yau kimanin watanni uku ke nan,” in ji kungiyar.

Ta kara da cewa “A saninmu, batun aiwatarwa bai kai ga teburin Mai girma Gwamna ba, Kwamared Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu), wanda ke nuna rashin son aiwatar da yarjejeniyar ko da a watan Afrilun 2026,” in ji ta.

Kungiyar ta bukaci gwamnati da ta aiwatar da yarjejeniyar gaba daya daga ranar 1 ga Janairu, 2026, wanda ya kunshi “dukkan karin girma, matakai, sauran alawus-alawus da kuma abubuwan da suka dace da ke cikinta.” Dangane da alawus-alawus na Ilimi, ASUU-AFUSTA ta ce ta gabatar da lissafin ma’aikatan ilimi 308 na 2014 zuwa 2021, da kuma ma’aikata 323 na 2022 zuwa 2024, a farkon 2025. Amma har yanzu Shuru ka keji.

“Duk da kokarin da kungiyar ta yi, gwamnatin jihar Kebbi ba ta biya kudaden alawus-alawus din ba,” in ji kungiyar.

Kungiyar ta yi nuni da basussukan da ba a biya ba tun daga shekarar 2016 zuwa 2025, tare da fitattun lokutan daga watanni shida zuwa watanni 31 a duk shekara. Ta kara da cewa atisayen bunkasar na shekarar 2025, wanda ya fara a watan Fabrairun 2026, ya rigaya ya ci bashin watanni bakwai.

Kungiyar ASUU-AFUSTA ta kuma lura da rashin aiwatar da karin albashin na shekara daga 2020 zuwa 2026, wanda ya haifar da basussukan har na watanni 42.

Sauran kudaden da ba a warware ba sun hada da bashin watanni shida na albashin N35,000 daga Oktoba 2023 zuwa Maris 2024, da kuma watanni 16 na bashin karin kashi 35% da 25% na albashin da ya shafi Satumba 2023 zuwa Disamba 2024.

Kungiyar ta ce watanni uku na basussukan daga mafi karancin albashi na 2024, wanda aka aiwatar a AFUSTA a watan Janairun 2025, har yanzu ba a biya su ba, tare da biyan bashin watanni 62 na albashin 2019 da ya biyo baya. Har ilayau ta kuma koka da rashin kammala aikin ingantawa na 2024, inda ta bayyana cewa tantance ma’aikata saboda karin girma na mukamin Reader da Farfesa daga ranar 1 ga Oktoba, 2024, har yanzu ba a tura su don tantancewar na wajen Jami’ar ba.

“Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i, Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio, dake Aliero ta nuna zumunci, nuna fahimta, tare da nuna kamun kai ga gwamnatin Kwamared Dakta Nasir Idris na nuna hakuri na tsawon lokaci ba tare tsunduma yajin aiki ba, bisa ga hakan Muna Jan hakalin Gwamnatin Jihar Kebbi na tabbatar da cewa ta warware wannan matasalar na ba da jimawa ba” in ji ƙungiyar.

“Mun yi imanin Malam Abdullahi Fodio, wanda ya tsaya kan bil’adama da adalci, ba zai taba farin ciki a matsayinsa na shugaba ba don ganin an yi wa al’ummarsa wannan magani da za a iya kaucewa.”

ASUU-AFUSTA ta ce ta yanke shawarar tura “dukkanin ka’idojin doka da ake bukata don ganin an warware duk wasu matsalolin biyan kakKokin da suka shafi mambobinmu.” Kungiyar ta bayyana cewa babban taronta na reshen zai gudana akwanan inda zata nemi izini don tsunduma yajin aikin Sai baba ta gani idan har gwamnatin Kebbi ta warware wannan matsalolin biyan kakKokin mambobinta.

“Sakamakon rashin kulawar da hukumomin da abin ya shafa suka yi don warware matsalolin biyan kakKokin mambobinta kungiyar, kungiyar ta yanke shawarar sake sanar da jama’a da sauran masu ruwa da tsaki Kan harakokin ilimi a Jihar cewa muna neman hanyar da ta dace kan duk batutuwan da suka shafi biyan kakKokin mambobinta,” in ji kungiyar.

Daga karshe “Idan har wadannan roko ba su haifar da sakamako mai kyau ba, duk hanyoyin da ake da su na aiwatar da wadannan bukatu, gami da bukatar daukar matakan yajin aiki na masana’antu (Total, Comprehensive and Indefinite Strike action) daga kungiyar ASUU ta kasa a taron majalisar zartarwa ta kasa mai zuwa da aka shirya gudanarwa a ranar 9-10 ga Mayu, 2026, za a gabatar da bukatar don tsunduma yajin aikin,” in ji ta.

AFUSTA
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya
  • Sulaiman
    Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari
  • Sulaiman
    Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana
  • Sulaiman
    Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili
AFUSTA
Umar Faruk Birnin Kebbi
+ posts Bio
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    An Cafke Matar Da Ta Binne Jariri Da Rai A Kebbi
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    Gwamnatin Kebbi Ta Ba da Ƙwangilar Gina Hanyoyi Kan Naira Biliyan 2.1
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    Sanata Adamu Aliero Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Tallafi Ga Ƙananan Hukumomi Takwas A Kebbi
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    Gidauniyar Sarki Salman Ta Rab Tallafin Abinci Ga Mutane 2,450 A Kebbi

MASU ALAKA

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF
Rahotonni

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin
Rahotonni

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026
Labarai

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 13, 2026
Next Post
Yadda Dalibin Jami’ar Jos Da Aka Sace Ya Samu Ƴanci Bayan Mako Biyu

Yadda Dalibin Jami'ar Jos Da Aka Sace Ya Samu Ƴanci Bayan Mako Biyu

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 13, 2026
NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026
Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

June 13, 2026
Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.