Za a gudanar da cikakken zama na biyar na kwamitin tsakiya na 20 na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) a birnin Beijing a watan Oktoba mai zuwa, kamar yadda yake kunshe a wata shawara da aka yanke, a yayin taron ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS da aka gudanar yau Alhamis.
Bisa babban tsarin ajandar cikakken zaman, ofishin siyasa zai gabatar da rahoton ayyukansa ga kwamitin tsakiya na JKS, kana za a yi nazarin muhimman batutuwa game da inganta cikakken tsarin ikon kai na jam’iyyar da ya kunshi komai da komai.
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS ne ya jagoranci taron na yau Alhamis, wanda har ila yau, ya yi nazari tare da fashin-baki kan halin da tattalin arziki ke ciki a yanzu, da kuma tsara yadda za a gudanar da ayyukan tattalin arziki a rabi na biyu na wannan shekara. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














