Iyalan mutane 176 da ‘yan ta’adda suka sace a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, sun sake roƙon Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kwara da su gaggauta ceto ‘yan uwansu, bayan kusan watanni shida da sace su.
Iyalan sun ce ‘yan ta’addan sun yi barazanar tilasta wa matan su aure su, yayin da za su kashe sauran mutanen da ke tsare idan ba a biya musu buƙatunsu ba.
Da yake magana da BBC Hausa, wani mazaunin Kaiama mai suna Abdul Ibrahim ya ce jama’ar yankin sun tara sama da Naira miliyan 155 ta hanyar gudummawa domin a sako mutanen, amma ya yi zargin cewa ‘yan ta’addan sun ƙi karɓar kuɗin fansar.
Ya ce iyalan sun bi duk hanyoyin da za su iya, har da yin zanga-zangar lumana, amma har yanzu ba a ceto mutanen ba.
Don haka ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen ceto su.
Shi ma wani jagoran al’umma, Suleiman Bukata, ya buƙaci gwamnati ta gudanar da irin aikin da aka yi kwanan nan wajen ceto ɗaliban Jihar Oyo.
A nasa ɓangaren, Sanata Adamu Aliero ya sake jaddada buƙatar kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.














