Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake jaddada kudirinta na inganta jin dadin malamai...
Read moreDetailsRundunar ’Yansandan Jihar Kano ta gayyaci dan takarar majalisar dokokin jihar mai...
Read moreDetailsBabban jirgin sama samfurin AG600 mai suna Kunlong da Sin ta kera a cikin gida, wanda ke iya tashi da sauka a kan doron kasa da cikin ruwa, ya kammala aikinsa na bana a Jiagedaqi da ke lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin. Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin wato AVIC ya bayyana a yau Litinin cewa, jirgin ya yi nasarar kammala ayyukan kai daukin gaggawa da na kare gobarar daji, na tsawon watanni 4 a sararin samaniya. Kuma yayin aikin na watanni 4, ya yi tafiye-tafiye domin sintiri sau 35, inda ya kwashe tsawon sa’o’i 100 na tafiya lami lafiya, ya kuma zubo da ruwa kimanin ton 390. Bisa la’akari da yadda yake iya shawagi a kusa da doron kasa kuma ba tare da gudu sosai ba, da karfinsa na daukar ruwa mai yawa da saukin sauya alkibla, jirgin ya nuna karfinsa na kai daukin gaggawa da kashe gobara a dazuka masu sarkakiya. Kasar Sin ce ta kera jirgin na Kunlong da kanta, domin biyan bukatun kasar na kashe gobarar daji da ayyukan ceto a cikin ruwa. Kuma shi ne irinsa mafi girma a duniya da ba na aikin soja ba, idan aka kwatanta da nauyin da yake iya tashi da shi. Nan gaba, jirgin zai shiga matakin aiki na yau da kullum, inda zai taimaka wa wani sabon samfuri mai karewa da kashe gobarar daji. (Fa’iza Mustapha)
Read moreDetailsSojojin Nijeriya sun yi nasarar kuɓutar da mutane da dama da ƴan...
Read moreDetailsAƙalla mutane da dama ne ake fargabar sun rasa rayukansu a ranar...
Read moreDetailsHukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta...
Read moreDetailsRundunar Ƴansandan Jihar Bauchi ta tabbatar da kisan wata tsohuwar shugabar mata...
Read moreDetailsHaɗin gwiwar hukumomin tsaro ana ƙasa, da suka haɗa da Sojoji da...
Read moreDetailsGwamnatin Jihar Yobe ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da aiwatar...
Read moreDetailsAƙalla mutane 28 ne aka tabbatar da mutuwarsu a daren ranar Talata,...
Read moreDetails© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.