ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Kama Miyagun Ƙwayoyi Na Sama Da Naira Biliyan 5

by Abubakar Sulaiman
4 weeks ago

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta sanar da samun nasarar cafke ɗumbin haramtattun ƙwayoyi da darajarsu ta haura naira biliyan biyar (N5bn) a tashoshin jiragen ruwa na ƙasar, tare da kama wani ɗan kasuwa da ke shirin tafiya birnin Milan na ƙasar Italiya ɗauke da hodar iblis a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, ya bayyana cewa an tare kayayyakin ne a tashoshin jiragen ruwa biyo bayan bayanan sirri da binciken haɗin gwiwa da aka gudanar a kan wasu kwantenonin da aka shigo da su, inda aka gano ɗimbin magungunan ƙwayoyi masu haɗari da suka haɗa da opioids da wasu kwayoyin da ba a amince da shigarsu Nijeriya ba.

A ɓangare guda kuma, jami’an hukumar sun cafke ɗan kasuwan ne mai suna Augustine Nnamdi, a daidai lokacin da yake ƙoƙarin shiga jirgin da zai tashi zuwa Milan na ƙasar Italiya, bayan da bincike ya nuna cewa ya ɓoye ƙunshin haramtattun ƙwayoyin a cikin kayansa da nufin yin safararsu zuwa nahiyar Turai.

ADVERTISEMENT

Hukumar ta bayyana cewa an tsare wanda ake zargin domin zurfafa bincike kan hanyoyin da yake amfani da su da kuma waɗanda suke haɗa baki da shi a cikin wannan haramtacciyar sana’a, domin gurfanar da su a gaban kotu.

Shugaban Hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya jinjina wa dakarun hukumar bisa tsayin daka da nuna ƙwarewa wajen toshe hanyoyin shigo da ƙwayoyi da fitar da su, yana mai sake nanata aniyar hukumar na fatattakar masu fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma hana Nijeriya zama matattarar safarar haramtattun kayayyaki.

LABARAI MASU NASABA

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto
  • Abubakar Sulaiman
    Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
Manyan Labarai

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci
Rahotonni

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya
Ra'ayi Riga

Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

October 30, 2026
Next Post
Ɗalibai Sun Yaba Wa Gidauniyar Dangote Kan Shirin Rabon Hannun Jari Kyauta

Ɗalibai Sun Yaba Wa Gidauniyar Dangote Kan Shirin Rabon Hannun Jari Kyauta

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

October 30, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

October 30, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

October 30, 2026
Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

October 30, 2026
Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

October 30, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.