Rundunar Ƴansandan Jihar Bauchi ta tabbatar da kisan wata tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar, bayan da wasu mahara da ba a tantance ko su waye ba suka kai mata mummunan hari da yayi sanadiyar mutuwarta.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa maharan sun farmaki matar ne a gidanta da ke yankin, inda suka yi mata raunuka masu tsanani da suka yi sanadiyyar mutuwarta kafin su tsere daga wurin.
Bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an ƴansanda sun garzaya inda abin ya auku domin shawo kan halin fargaba da al’ummar yankin suka shiga, tare da ɗaukar gawar matar zuwa asibiti domin gudanar da binciken likita kafin miƙa ta ga iyalanta domin yi mata jana’iza.
Rundunar ta bayyana cewa Kwamishinan Ƴansandan Jihar ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi cikin gaggawa a sashin binciken manyan laifuka (CID), da nufin gano ainihin waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki da kuma manufar da ta sa suka kashe ta.
A ƙarshe, rundunar ƴansandan ta yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankulansu su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu, tana mai buƙatar duk wanda ke da wani sahihin bayani da zai taimaka wajen gano maharan da ya gaggauta sanar da jami’an tsaro.













