ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

“Lokacin Afirka” Da Kasar Sin Ta Ware Da Bai Taba Sauyawa Ba Tsawon Shekaru 36

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Afirka

Kasar Sin na kiyaye wata al’ada ta tsawon shekaru 36 a fannin diflomasiyya, wato a farkon kowace shekara, ministan harkokin wajen kasar kan yi ziyararsa ta farko a kasashen waje a nahiyar Afirka. A wannan shekara ma haka za a yi, duba da cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, Mr. Wang Yi, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, zai ziyarci kasashen Habasha, da Somaliya, da Tanzaniya, da Lesotho, bisa goron gayyatar da aka ba shi, tsakanin ranekun 7 zuwa 12 ga Janairun nan, kuma zai halarci bikin kaddamar da “Shekarar cudanyar al’umma da musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka”, a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Amma me ya sa ministocin harkokin wajen kasar Sin suka yi ta kiyaye wannan al’ada? Muna iya gano amsar tambayar daga zancen da Mr. Wang Yi ya yi lokacin ziyararsa a Afirka a farkon bara. A yayin zantawa da shugabar kasar Namibia Netumbo Nandi-Ndaitwah, Wang Yi ya ce, ”Ta hanyar kiyaye wannan al’ada ta kai ziyararmu ta farko a kasashen Afirka a farkon kowace shekara, muna son shaida wa duniya cewa, a duk irin sauye-sauye ko yanayin da ake ciki a duniya, kullum kasar Sin tana kasancewa aminiyar da kasashen Afirka suke iya amanna da ita, da zama kawar da suke iya dogaro da ita a kokarinsu na tabbatar da ci gabansu, haka kuma kasa ce da ke mara musu baya a dandalin kasa da kasa. ”

Yadda kasar Sin ta furta ke nan, kuma hakan take aikatawa.

ADVERTISEMENT

In mun yi nazari, za mu gano cewa, kamfanonin kasar Sin sun sa hannun gina ko gyara layin dogon da tsawonsu ya zarce kilomita dubu 10 da hanyoyin mota kusan kilomita dubu 100 da gadoji kusan dubu da tashoshin jiragen ruwa kusan dari da sauran nau’o’in ababen more rayuwa masu yawa a kasashen Afirka. Har wa yau, kasar Sin ta dade da kasancewa daya daga cikin kasashen da suka fi samar da kudaden jari ga Afirka, kuma a cikin shekaru biyar da suka wuce, matsakaicin kudaden jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a Afirka ya zarce dala biliyan 3 a mizanin shekara-shekara. A kokarin taimaka wa kasashen Afirka wajen kara fitar da kayayyakinsu ketare da kuma more babbar kasuwarta, kasar Sin ta kuma cire harajin kwastam a kan dukkanin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diplomasiyya da ita. Lallai, duk wadannan sun shaida cewa, kasar Sin aminiya ce da kasashen Afirka suke iya dogaro da ita a kokarinsu na tabbatar da ci gabansu, wanda hakan ya zama dalilin kyawawan nasarorin da suka cimma a hadin gwiwarsu.

Idan ba mu manta ba, a watan Satumban shekarar 2023, lokacin da wakilin kungiyar tarayyar Afirka ya zo wajen taron kolin kungiyar G20, wurin ya rude da tafi. Lallai kasar Sin ita ce ta farko da ta bayyana goyon bayanta ga shigar da kungiyar tarayyar Afirka a matsayin mambar kungiyar G20, kuma matakin da ya taimaka ga kara fitowa da muryar kasashen Afirka a fagen duniya. A hakika, kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka a kan goyon bayan kasashen Afirka da ma tarayyar Afirka da su kara taka rawarsu a harkokin duniya da na shiyya shiyya, da kuma nuna goyon baya ga biyan bukatun kasashen Afirka a batun yi wa kwamitin sulhun MDD kwaskwarima. Baya ga haka, kasar Sin ta kuma yi kira da a kara wakilcin kasashen Afirka a hukumomin hada-hadar kudi na tsakanin bangarori da dama. Lallai hakan ya shaida cewa, kasar Sin har kullum ta kasance kasar da ke mara musu baya a dandalin kasa da kasa.

LABARAI MASU NASABA

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Sin Na Daukar hakikanan Matakan Gina Kyakkaywar Makomar Al’ummun Sin Da Afirka Ta Bai Daya

Shekarar 2026 ita ce ta cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, haka kuma ta kasance “Shekarar cudanyar al’umma da musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka” irinta ta farko. Cudanyar al’ummunsu ita ce tushen huldar Sin da kasashen Afirka. A kwanakin baya, Paul Zilungisele Tembe, masanin harkokin kasar Sin daga kasar Afirka ta Kudu ya yi nuni da cewa, yanzu haka hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta shiga wani babban mataki, musamman ta fannonin siyasa da tattalin arziki. Sai dai idan babu fahimtar juna mai zurfi ta fannin al’adu, to, da wuya su zurfafa aminci da juna. Yadda aka kaddamar da shekarar cudanyar al’umma da musayar al’adu a tsakaninsu, zai taimaka ga inganta fahimtar juna a tsakaninsu, wanda hakan zai kiyaye dauwamammen ci gaban huldarsu. Shekarar 2026 ta kuma kasance shekarar da kasar Sin za ta fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, kuma bisa ga yadda ake hada shirin nan na kasar Sin tare da shirin ajandar kasashen Afirka ta shekarar 2063, Sin da kasashen Afirka za su karfafa niyyarsu ta samar da kyakkyawar makomarsu ta bai daya.

A daidai wannan sabon mafari na shekarar 2026, ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a kasashen Afirka, tabbas za ta karfafa aiwatar da sakamakon taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka, da karfafa koyo daga juna a tsakanin Sin da Afirka a matsayin masu manyan wayewar kai guda biyu, da kuma kara sanya sabon kuzari ga gina al’ummar Sin da Afirka ta dukkan fannoni mai makoma ta bai-daya a sabon zamani. (Lubabatu)

Afirka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi
Afirka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Ra'ayi Riga

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Sin Na Daukar hakikanan Matakan Gina Kyakkaywar Makomar Al’ummun Sin Da Afirka Ta Bai Daya
Ra'ayi Riga

Sin Na Daukar hakikanan Matakan Gina Kyakkaywar Makomar Al’ummun Sin Da Afirka Ta Bai Daya

June 19, 2026
A Yi Watsi Da Wannan “Mummunan Teburi”
Ra'ayi Riga

A Yi Watsi Da Wannan “Mummunan Teburi”

June 18, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Daƙile Harin Fashi Da Makami A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

June 25, 2026
EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

June 25, 2026
Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.